DABAIBAYIN DA KE CIKIN SABON FASALIN MASARAUTAR KANO – BELLO MUHAMMAD SHARADA

0
587

Daga Bello Muhammad is

Majalisar dokoki ta jihar Kano ta yi karatu na daya dana biyu dana uku a cikin awa 72 sun gyara dokar fasalin masarautun Kano. Shugaban majalisar da kansa ya dauki dokar ya tafi gidan gwamnan Kano da la’asar lis ya kai masa. Zuwa yanzu gwamna Ganduje ya saka wa wannan dokar hannu kamar yadda ya yi alkawari zai yi in ta iso gare shi.

Bisa fasalin ‘yan majalisa. Yadda suke so masarautun Kano su kasance shi ne: Akwai tsohuwar masarautar Kano karkashin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II tana da kananan hukumomi goma sune Kano Municipal da Fagge da Nasarawa da Gwale da Tarauni da Dala da Minjibir da Ungogo da Kumbotso da Dawakin Kudu. Sannan sai Masarautar Rano wacce ta kunshi Rano da Bunkure da Takai da Kibiya da Sumaila da Doguwa da Kiru da Bebeji da Kura daTudun Wada.

Sauran masarautun guda uku sune: Masarautar Bichi da Gaya da Karaye. Bichi tana da kananan Hukumomi guda tara sune Bichi da Bagwai da Shanono da Tsanyawa da Kunci da Makoda da Danbatta da Dawakin Tofa da Tofa. Ita kuma Masarautar Karaye ta kunshi wadannan kananan hukumomin Karaye da Rogo da Gwarzo da Madobi da Kabo da Rimin Gado da Garun Mallam. Masarautar Gaya ta kunshi Gaya da Ajingi da Albasu da Wudil da Gezawa da Gabasawa da Warawa

Duk da kotu ta yi umarnin a jingine duk wannan shirin, gwamna Ganduje ya nada Alhaji Aminu Ado Bayero, Wamban Kano a matsayin sabon sarkin Bichi. Sarkin Gaya da sarkin Rano da Sarkin Karaye, wadanda a wancan tsarin hakimai ne.

Mutanen Rano da Karaye da Gaya da Bichi za su ji dadi sosai an daga darajar kasashensu. Mutanen wannan yankunan sun dade suna da wannan burin, a yanzu ba nema suka yi ba, aikin ‘yan siyasa ne da suke son biyan wata bukatarsu ya biyo ta nan.

Da Rano da Karaye da Gaya suna da tarihin sarakai, amma a tarihin nasu ikonsu bai wuce inda wadannan garuruwan suke ba. Rano iyakarta Rano. Gaya iyakarta tsohuwar Gaya. Matukar Karaye a Karaye take. Haka Bichi. Wannan sabon fasalin ya kwace ikon ainihin wani yanki na kasar Kano ne ya danka shi a hannunsu. Abin da sai an yi yaki da zub da jini a tarihin baya sannan su kai gare shi, a ruwan sanyi sun same shi, ba gumi ba zufa.

Har da wannan sabon fasalin, karo na uku kenan da aka raba masarautar Kano. Marigayi gwamnan Kano Muhammadu Abubakar Rimi ya yi irin haka a shekarar 1980, Janar Babangida a shekarar 1992 ya raba Kano gida biyu, Kano da Jigawa. Hakan ya fitar da sarakunan Hadejia da Kazaure da Ringim da Dutse da Gumel daga Kano. Sai kuma yanzu da gwamna Ganduje ya sake daga darajar Rano da Gaya da Karaye, har kuma da Bichi.

Ni bani da ra’ayin a yaga masarautar Kano. A ganina babu fa’ida yin haka a yanzu saboda dalilai, kamar haka.

1. An yi wannan shiri ne domin a rage karfin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ko kuma a warware rawaninsa. In mutum daya ya yi laifi, bai dace a wargaza tarihi da kwarjinin masarautar Kano ba. Manyan masarautu a duniya masu tsohon tarihi irin na Kano kamar Ingila da Belgium da Japan da Thailand ba wanda ya ballagazar da su. Sarakansu suna yin magana su saka baki a sha’anin mulki da tafiyar da kasa, wannan bai sa a keta musu masarauta don a huce haushi.

Abu na biyu, yadda aka yi fasalin ba zai samar da hadin kai da biyayya ba a tsakanin hakiman da sarakan. Zai iya kawo rashin jituwa da yamutsi. Misali, za a samu sabani in ka dauki Hakimin Dambatta wato Sarkin Bai da hakimin Dawakin Tofa wato Madakin Kano ka maida su karkashin sarkin Bichi. Su biyun fa suna cikin masu nada sarki a Kano. Haka za a samu gagarimin sabani in ka ce Makaman Kano kuma Hakimin Wudil ka mayar da shi karkashin Sarkin Gaya. A tsari na siyasa wajibi ne a ji ra’ayin mutanen sauran garuruwan da za a yanke su daga Kano a maida su karkashin sarakan Rano da Gaya da Karaye da Bici. Ita ma majalisa sai ta shirya zaman sauraron jin ra’ayi, kafin zartar da irin wannan kuduri mai muhimanci da tasiri a rayuwa da tarihin Kano. Ba a yi hakan ba. An yi yadda bature da soja suke yi in za a su yi doka, ba ruwansu da wanda zata shafa.

Abu na uku, Jihar Kano tana kukan rashin kudi kuma akwai sabgogi da suka zama tilas gwamnati ta kula da su, kamar ilimi da lafiya da noma da kasuwanci, duk aka ajiye su, aka dauko sabon aikin gina sabbin masarautu hudu. In ka yi sabbin masarautu, zaka kwashi kudin jiha dana LG ka gina fada, ka kara overhead, ka dauki ma’aikata, kaga da gangan kai da kake kukan ba kudi, ka kara wa kanka jidalin kudin akan abin da ba lalura bane, akan al’ummar Kano.

Abu na hudu, wannan sha’ani an dabaibaye shi da harkar siyasa. Kusan duk wani dan Kwankwasiyya yana sukan wannan sabon fasalin. Haka kuma akasarin ‘yan Gandujjiya suna goyon bayan gwamnati. A irin wannan yanayin komai kyawun niyyar Ganduje, a gurin PDP ba alheri ba ce, mai suka kuma komai hujjarsa a wajen ‘yan Ganduje makiyi ne. Akwai tsoro anan. Nan da shekara hudu in an samu canjin gwamnati, za a iya maida wadannan masarautu yadda suke kafin wannan fasali. Me yiwuwa kuma an rinka yin wannan sabatta-juyatta kenan, duk lokacin da aka samu canjin gwamnati, a samu sauyi na masarautu ko sarakai.

Abu na biyar shi ne, wannan fasalin zai haifar da sabuwar rashin jituwa a tsakanin ‘yan Birni da mutanen karkara. Dama a birni suna dan kauye ya rusa, idan wani dan birni ya zo ya yi kwaskwarima, sai a kulla gaba a tsakani. Irin wannan zai shiga har siyasa da sha’anin mulki da lamuran addini da ayyukan raya kasa. Kusan hakan tana faruwa a tsakanin Daura da Katsina da kuma Hadejia da Dutse da wasu misalai irin haka da yawa.

Abu na shida tsarin masarautun a dunkule yana da fa’ida ga baki na Najeriya da wajenta. Hawan Daba wanda yake shi ne kadai irinsa a duniya zai sami tasgaro. Ya kamata ne a inganta shi ba a rusa shi ta yadda zai rika jawo wa Kano kudi da kwarjini. Matsayin da majalisar dinkin duniya ke son saka harkar Hawan Daba, za a saryar da shi. Idan an tabbatar da keta masarautun to Sarki Muhammadu Sanusi II ya kafa tarihi a matsayin shi ne sarkin Kano na karshe, daga shi ta rushe, shi kuma Gwamna Ganduje zai kafa tarihin shi ne ya yi wa sarautar Kano ayaga.

Nasiha ta kawai ga gwamna, shi ne akwai mutuwa, akwai rashin lafiya, akwai gama wa’adi, akwai kotu, yadda ya samu mulki kada a rika siyasa irin ta Machievilli. Kano muna da al’adun siyasa da koyarwar addini da salonmu na jagoranci, a maida hankalin al’umma ga abin da ya yafi damunsu matuka.

Leave a Reply