Yau na kara tabbatar da rashin hankali da jahilcin wasu daga cikin yaran Kwankwasiyya

0
472

Daga Haji Shehu

Lallai muddin Kwankwasiyya zata cigaba da tafiya da marasa kwakwale, to tabbas babu inda tafiyar zata karkare sai rashin nasara da kuma kara samun koma baya.

Banda rashin ilimi da toshewar kwakwale, haka kawai wasu su kirkiro karya domin rage darajar tafiyar siyasar ku, ku kuma ku kasa gane salon takun su, suna jefowa kawai kuka cabe.

Labarin da ake yadawa akan cewar Isa Ali Pantami ne ya fada, labarin karya ne domin na bibiyi tafsiran Isa Ali Pantami na azumin bana banji inda ya fadi maganar ba. Haka kuma na tuntubi makusantan shi domin sanin sahihancin zancen, suma sunce gani kawai sukayi ana watsawa a shafukan sada zumunta.

Ta inda naga toshewar kwakwalen yan Kwankwasiyya shine, yadda sukayi ca akan Isa Ali Pantami suna rugawa iyayen sa ashariya ba tare da duba makomar siyasar su awajen dumbin mabiyan Isa Ali Pantami ba.

A iya nazari da tunanina, wannan labari wasu kwararru ne suka kirkireshi domin tunzura Marasa hankali na Kwankwasiyya, da zummar neman rage daraja da mutuncin Kwankwasiyya a idon mabiya Isa Ali Pantami. Kuma tabbas sunyi nasara domin Isa Ali Pantami da Iyaten sa sun sha zagin kare dangi agun yan Kwankwasiyya, su kuma mabiya Isa Ali Pantami wadanda suke ganin Kwankwasiyya da mutunci sun dawo daga rakiyar ta.

Leave a Reply