DUNIYA KUNDI: Ko kun san mutumin da ya fara kirkirar Na’urar Tangaraho (Telephone).

0
286

Daga Haji Shehu

Kamar ko wacce Lahadi, yau shirin Duniya Kundi zaiyo linkaya cikin rayuwar mutumin da ya fara kirkirar Na’urar Tangaraho domin tsakuro muku kadan daga rayuwar sa.

Alexander Graham Bell dan kasar Amurka shine mutumin da ya fara bincike tare da samarda Na’urar da zata sada mutanen dake nesa cikin kankanin lokaci. An haifi Alexander a shekarar 1847 ya rasu a shekarar 1922.

A shekarar 1874 Alexander ya fara bincike kan fasahar da zata sada mutanen dake nesa cikin kankanin lokaci, inda ya fara bincike kan samarda (Telegraph) hanyar da zata sadar da zumunta ta tsakanin wuraren dake da tazara cikin kankanin lokaci. Alexander tare da abokan aikinsa sunyi ta fadi tashi wajen cigaba da fadada bincike domin saukake sadarda zumunta a duniya.

A shekarar 1876 Alexander ya yi nasarar kirkirar Na’urar Tangaraho (Telephone) mai cin matsakaicin zangon sada zumunta, Alexander yayi ta fadada binciken wajen fadada Na’urar tangaraho ta yadda zata ke cin nisan zango, ya kuma yi nasarar fadada ta a shekarar 1892 inda ya yi gwaji daga garin New York zuwa Chicago.

Mu tara daku ranar Lahadi domin samun wani shirin na Duniya Kundi. Zaku iya aiko da sakonku ta wannan Number 070 63177943

Leave a Reply