BAYANIN YADDA SHEIKH DR ISA ALI PANTAMI YA TAIMAKI TSARON NIGERIA – DATTI ASSALAFIY

0
2001

Daga Datti Assalafiy

Wannan jawabin yana matsayin mayar da raddi ne ga mutanen banza da suke yiwa Malam Isah Ali Pantami batanci cewa tun daga lokacin da shugaba Buhari ya bashi mukamin shugaban NITDA malam yayi shiru akan matsalolin Nigeria, wai yana ji yana gani ana kashe mutane amma yayi shiru baya cewa komai saboda gwamnati ta bashi mukami.

To bari kuji ya ku wadanda suke yiwa Malam suka da batanci, kuje ku nemi darasin tafsirin Qur’ani da ya gabatar kwana uku da suka gabata, wato ranar 6 ga wannan wata na Ramadan, wani bawan bawan Allah ne ya rubuto tambaya yake cewa Malam menene amfani Sarakun gargajiya? shi a gurinsa basu da wani amfani ya kamata a rushe su gaba daya.

Bayan Malam Isah Ali Pantami ya karanta tambayar sai ya fara bashi amsa da cewa babbar magana, bai kamata a rushe sarakunan gargajiya ba, domin suna da matukar amfani da tasiri, Malam ya kawo tarihin Sarkin gargajiya na Kasar Habasha, Sarki Annajashi wanda yayi zamani da Annabi Muhammad (SAW), Malam ya fadi adalcin wannan Sarki wanda ba ma musulmi bane sai a karshen rayuwarsa ya musulunta, sannan sai Malam ya buga misali da mai alfarma Sarkin Musulmai Muhammad Sa’ad Abubakar domin ya bayyana muhimmancin sarautun gargajiya.

Malam yace a shekaran da ta gabata (2018) lokacin da ake cikin wani mumman halin yanayin tsaro na rikicin fulani makiyaya da manoma, ana ta kashe kashe musamman a yankin arewa ta tsakiya, Dr Isah Ali Pantami yace abin ya dameni, na rasa yadda zanyi, sai na dauki waya na kira Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar, nace masa rankayadade babu yadda za’ayi ne akan rikicin fulani?, sai yace mu mu samu lokaci mu zauna.

Dr Isah yace sai na tafi Sokoto muka zauna da Sarkin Musulmi, muka tattauna sosai, sai muka samu matsaya cewa burinmu na kawo karshen rikicin fulani makiyaya ba zai cika ba har sai an nemi iznin gwamnati, akace aje yi, Sarkin Musulmi ya hada Dr Isah Ali da shugaba kungiyar Miyetti Allah na kasa Alhaji Kirowa daga jihar Kebbi, da Sakatarensa Malam Usman daga jihar Yobe, ya kirasu suka tafi Sokoto gaban Mai alfarma Sarkin musulmi aka zauna aka tattauna.

Shugabannin Miyetti Allah suka fadi korafe korafensu cewa ga yadda ake zaluntar mutanen su, Sultan yace musu ya za’a magance matsalar? aka zauna, Dr Isah Pamtami yace sunyi meeting da shuhanannin Miyatti Allah a Sokoto da Abuja a kalla ya kai sau ashirin domin a lalubo hanyar da za’a kawo karshen rikicin fulani a Kasarnan.

Dr Isah Ali Pantami yace wallahi da kudin aljihunsa, shima Sarkin Musulmi da kudin aljihunsa haka suke cirewa su hada su baiwa shugabannin Miyatti Allah don su biya kudin jirgi daga garuruwansu suje Sokoto ko Abuja a hadu a tattauna, har suka amince suka tattaro dukkan mutanensu a cikin kowace jihohin Nigeria 36 suna wayar da kan fulani makiyaya cewa ko an tabaku kada ku rama, ku gaya mana zamu kaiwa hukuma za’ayi hukunci.

Sukazo suka tabbatar da cewa sunyi alkawari daga yau indai mutum bafulatani ne a Kasarnan Nigeria yake tare da su Miyatetti Allah, to ko mai aka masa ba zai dauki mataki ba, sai dai ya kawo kara wajen hukuma kuma hukuma tabi kadin abin.

Dr Isah Ali Pantami yace yanzu ka kara jin rikicin fulani makiyaya sunyi kashe kashe ya faru? To da Sarkin Musulmi akayi, imba an fada ba waye yasan an yi haka?, amma kun sake jin an zalunci fulani sun rama?, an zaluncesu a Mangu sun rama? inda a da ne da sun rama, daga ni Isah Ali Pantami sai Malam Nuhu Ribadu sai Shehu Buba da Sarkin Kano Sununi haka aka hada kai aka magance matsalar rikicin fulani a kasarnan ba wanda ya sani.

Imba yau ba ban taba fada wa kowa ba, kuma imba don albarkacin Sarkin musulmi ba da bamu samu damar zama da shugabannin fulani an magance matsalar ba, farko ni na fara nemansu amma kin saurarana sukayi sai da na tuntubi Sarkin Musulmi, don haka kuskure ne ace wai a rushe Sarakunan Gargajiya, suna da matukar amfani.

Ina wadanda suke cewa Malam yayi shiru ana kashe kashe a Nigeria, kunga hanyar da yabi ya magance matsalar rikicin fulani makiyaya a daidai lokacin da manyan makiya zaman lafiyar Nigeria irinsu TY Danjuma suke kira ga jama’arsu cewa su dauki makami su kare kansu don a hadu a hargitsa Kasar, Malam Isah Ali ya magance matsalar duk cikinmu ba wanda ya sani sai yanzu, gashi yanzu haka a yankin da TY Danjuma ya fito ‘yan uwansa Jukunawa da Tibabe sun koma suna yakar junansu, rikicin fulani ya kare.

Sati biyu da ya gabata, wasu kabila a karamar hukumar Bassa jihar Pilato suka farwa fulani makiyaya suka kashe shanun fulani kusan dari hudu, shine rubutun da nayi na karshe mai taken DOLE A YIWA FULANI MAKIYAYA ADALCI na saka video da hoto na ta’addancin da aka yiwa shanun fulani, shine sai aka samu wasu tsinannu suka yi reporting rubutun Facebook suka dakatar dani daga yin posting, comment, like da inbox chart na sati guda.

Inda ace Dr Isah Ali Pantami bai jagoranci yin sulhu da fulani makiyaya ba aka musu wannan ta’addancin a Bassa wallahi da sai sunyi gayya sun dau fansa, amma har zuwa yau basu rama ba saboda sulhu, Malam Isah Ali Pantami yayi abinda dukkan hukumomin tsaron Nigeria masu rike da makami suka gagara yi cikin kankanin lokaci, kuma da kudin aljihunshi.

Sannan rikicin Masu garkuwa da mutane wanda ya addabi jihohin Zamfara, tun da aka fara azumin watan ramadan na wannan shekara kullun sai Malam yayi magana a kai, kuma sai yayi addu’ah na neman shiriya ga wadanda suke aikata ta’addanci, hatta wadanda suke jin dadi ana ta’addancin Malam yana musu addu’ah, duk wanda yake sauraran tafsirinsa zai tabbatar, kunga ashe Malam baiyi shiru ba don ana kashe mutane, kuma a sirrance ba mu san matakin da yake bi ba, duk da na san Malam ba mutum bane mai shiga hurumin da bai shafi aikinsa ba, mutanen banza ne kawai marassa adalci suke zaginsa akan haka.

Don Allah ‘yan uwa daga yanzu duk wanda kuka ga yana kalubalantar Malam Isa Ali Pantami akan wai yayi shiru ana kashe mutane a Nigeria to ku nuna mishi wannan rubutun, kuma kuce yaje ya tambayi Sarkin Musulmi da shugabannin Miyetti don a tabbatar, shigar Malam cikin gwamnati alheri ne babba, ba gwamna ba nan gaba shugaban Kasar Nigeria muke fatan ya zama da ikon Allah.

Yaa Allah Ka tsare mana Malam Isah Ali Pantami, Ka kara masa taimako da nasara cikin dukkan lamarinsa Amin.

Leave a Reply