Yau Shekara 8 Da Kashe Gaddafi Shugaban Kasar Libiya – Datti Assalafiy

0
526

Daga Datti Assalafiy

Kalaman Mu’ammar Gaddafi ( marigari )

Ba zan taba gudun hijra zuwa wata kasa ba, an haifeni a nan kasar Libya, kuma anan zan mutu. Wannan kasar hamada ce kuma na juyata zuwa dokar daji, inda komai zai iya girma, ya rayu.

Babu wanda zai so kasar nan fiye da ‘yan Kasar. Idan Iropiya da Amurka sun ce suna sonku to ku kula, suna son arzikin kasarku ne, arzikin man fetur ne suke so amma ba mutanen ba, suna tayaku fada da ni, amma na fiku hankali dan ina fada dasu, don su suna fada da ku ne, dan ci gaban da za ku yi nan gaba.

Sako na gareku ‘yan Libya shi ne, Amurka na tayaku ku kashe ni, amma zaku biya diyyan mutuwata, saboda za ku shiga wahala bayan mutuwata. Sakona gareku mutane Amurka da Yurop shi ne za ku kashe ni, amma ku shirya fada da ta’addanci da ba zai taba karewa ba. Kafin ku ankara, jahilci da ta’addancin ku zai bude maku kofar halaka.

GADDAFI ya fadama gwamnatin Najeriya da ta Ingila su rabu biyu, sabida Hausa/Fulani ( Musulmai ) Yoruba ( Kiristocin su ) da ‘yan Biyafara/Inyamurai su zauna a mastayin makwaftan kasa.

‘Ya na da kyau mu dubi wadannan dalilai guda 16 da suka sa aka kashe marigayi
COL. GADDAFI da zan kawo maku kamar haka:-

1. Ba a biyan kudin wutan lantarki a Libiya, kyautace ga ‘yan kasan.

2. Gwamnati ba ta karban riba, idan ta baka rance, bankuna a Libiya ba a karbar riba a ka’ida.

3. Gidaje an barsu kyauta domin jama’a a Libiya. Gaddafi sai da ya yi alwa’shin sai ya gina ma kowa Gida kafin ya gina ma iyayensa.

4. Duk wanda zai yi sabon aure a Libiya za a rinka bashi dalar amurka 60,000 ($60,000) Dinars (US$50,000) daga aljihun gwamnati domin sayan kayan daki.

5. Harkar Ilimi da kiwon lafiya kyauta ne a Libiya, kafin zuwan Gaddafi, kashi 25% daga cikin yan libiya kadai sukeda ilimi, amma Bayan zuwan sa an sami kaso 83% cikin 100 masu ilimi.

6. Ana tallafawa manoma a lokacin Gaddafi Libiya, sannan ana basu gwanaki da gidanjen kiwo, kayan noma, hatsi da dabbobin kiwo duk kyauta ne.

7. A Libiya basa iya samun ilimi da magani, gwamnati ta samar masu daga kasashen waje.

8. Gaddafi Libya, ta siyo motocin gwamnati domin tafiye-tafiye. Naira 50 ake biya zuwa ko ina a fadin kasar.

9. Litar man fetir a Libiya naira $0. 14

10. Ba’a bin kasar Libiya bashi, hasalima gwamnati ta Libya ta ajiye kudi a asusu har kimanin bilyan $150.

11 Idan mutum ya gama jami’a bai samu aiki ba, Gaddafi na biyan kudin wata har sai ya sami aiki.

12. Ana rabon kudin arzikin man kasar kai tsaye daga bankin yan kasan.

13. Idan mace ta haifu, za’a rika biyan albashi ma jaririn, dalar amurka $5,000 har ya girm

14. Manyan biredi guda 40 a Libya $ 0.15

15. Kashi 25% na yan libiya suna da shaidar gama digiri

16. Gaddafi yafi kowa aiki a shugabannin duniya. Shine ya maida hamada zuwa tsungurmin daji. Shi sanannen shugaba ne, daya gina matatun ruwa gaba dayan kasar Libya, idan za a kirashi mai mulkin kama- karya, to ban san mulikin dimukuradiyya ya ke ba.

Fassarawa daga turanci zuwa harshen Hausa Sufiyan A. Y. Burtuwa

 

Leave a Reply