YADDA KUNGIYAR KWANKWASIYYA TA KE NEMAN ZAMA ANNOBA A KASA!

0
913

SHARHI: Daga Sheikh Habibullah Al-kanawy

Kamar yadda aka sani, kungiyar [Kwankwasiyya], darika ce ta mabiya tsohon gwamnan Jihar Kano, Eng. Rabi’u Musa Kwankwaso.

Kuma akasarin membobinta matasa ne masu jini a jika. Wadanda su ka ginu kan tsattsauran ra’ayi da rashin kunya a fage irin na Siyasa da al’amuran al’umma.

Duk mai nazari da bibiyar ayyukan membobin wannan kungiya, zai shaida cewa ba sa ganin kima da darajar kowa a wannan kasa face madugunsu.

Haka Kuma duk wani abu da zai kawo cikas ga tafiyarsu ko ya dakushe wata manufa tasu komai kyansa to su baki ne wulik! A wurinsu. Kuma sai sun yi damarar ganin sun munanta shi domin al’umma su ki shi.

Jama’a za ku yarda da wannan idan ku ka yi duba da zaben baya da aka gudanar a Jihar Kano, la’akari da yadda su ka fiddo da hotunan rikice-rikice da su ka faru a kasashen waje su ka Kuma dangantasu da cewa a Jihar Kano ne. Saboda kawai sun fuskanci manufarsu ba za ta kai ga cimmuwa ba sai sun yi haka.

Haka zalika, ku yi duba da abubuwan da su ke faruwa yanzu haka a Jihar Kano kan batun dokar karin masarautu da majalissar dokokin Jihar Kano ta yi. Gaba daya membobin wannan darika ta [Kwankwasiyya] sun hau kan wannan Batu sun yamutsa shi.

Sun haddasa rashin jituwa tsakanin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammad Sunusi na biyu da Mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, saboda bakar adawa da kiyayyar da su ke yi masa.

Sun kauda kansu kan alkhairin da ke tattare da wannan kari na masarautu da aka samu, sun shigar da Siyasa ciki sun sauyawa batun kamanni da siffa.

Sun kira sabbin Sarakunan da kalmomi kala-kala na rashin ladabi da girmamawa. Sun yi wa mai Martaba Sarkin Kano famfo ya na ganin Mai girma gwamna matsayin tamkar makiyinsa.

Duk kuwa da cewar al’ummar Jihar Kano ne su ka kai koken neman wannan kari na masarautu gaban majalissar dokokin Jiha.

Ita kuma ta yi karatu na daya da na biyu har zuwa na uku ta kuma rattaba hannu akai. Daga bisani aka kaiwa Mai girma gwamna ya Sanya hannu saboda amsa bukatun al’umma da Kuma duba muhimmnacin hakan.

Mu fahimci cewa, ko a iya hawan Sallah! Al’ummar Jihar Kano su na yin hasarar dumbin dukiya marar kidayuwa a sanadiyyar barayi da cinkoson al’umma ya ya yin hawan salla saboda duk girman Kano Masarauta daya ake da ita dole al’umma su taru domin kallon hawan Sallah!

Amma yanzu wanna Karin masarautu da aka samu zai taimaka wajen rage cinkoso ya yin hawan Sallah, duba da yadda wasu za su yi Gaya, wasu su tafi Karaye, wasu su je Bichi, wasu Kuma su zauna a cikin Kano.

Kenan hakan alkhairin ne babba ga al’ummar Jihar Kano, Amma duk wannan Yan Kwankwasiyya sun sa kafa sun shure, sun koma zage-zage da neman kawo bace kan lamarin.

Haka nan kuma, hatta Malaman addini ba su kyale ba, duba da yadda su ke furta munanan kalamai kan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Shaik Isah Ali Fantami.

Wasu daga cikinsu zaginsa su ke ta uwa ta uba, wasu kuwa sun ma yi ikirarin daukwar rayuwarsa ya bar Duniyar ma gaba daya. Domin sun ce sai sun kashe shi.

Kenan, a iya cewa wannan kungiya ta [Kwankwasiyya] mazahabar Siyasa ce da in ba ayi a sannu ba, da iyuwar Kila ta zame wata Annoba a wannan kasa.

Duba da yadda ba sa shakkar cin mutuncin duk wani mai mutunci, ba sa Kuma kyamar aibata duk wani Wanda ya saba da ra’ayinsu ko na Mai gidansu Musa Kwankwaso.

Sai Kuma gashi har ma barazana da ikirarin kisa su ka fara. Saboda tsattsauran ra’ayi da aka gina su akai.

Da wannan na ke ba wa gwamnati shawara, da ta Sanya ido sosai kan ayyukan wannan kungiya ta [Kwankwasiyya] da ayyukansu.

Domin idan mu ka yi duba da abubuwan da su ka faru a baya, kungiyoyi masu nasaba da addini kamar: Tatsine, da Boko Haram da Shi’a, an gina mabiyansu kan tsattsauran ra’ayi da Kuma biyayya ta a mutu ga jagororinsu.

To irin salon da Kwankwasiyya ta daukwa kenan, wato: tsattsauran ra’ayi da Kuma biyayya ta amutu ga madugunsu, Rabi’u Musa Kwankwaso.

Dan haka, dole mu yi nazari a kai, ka da nan gaba su zame mana Annoba. A duba iyuwar sa musu ido, duba da yadda su ke barazana da ikirarin za su kashe Shaik Isah Ali Fantami da cin mutuncin gwmanatin Jihar Kano da sauran mutane masu daraja.

Leave a Reply