ABUBUWA 12 GAME DA BINDIGAR. AK-47

0
830

Daga Bashir Abdullahi El-Bash

(1). Wanda ya kera ta, dan kasar Rasha ne sunansa Mikhail Kalashnikov. An haife shi ne a shekarar 1919.

(2). Ya fara tunanin kera ta ne a shekarar 1942 bayan da ya samu wani rauni a yakin duniya na II aka kai shi wani asibiti jinya. Sai wasu daga cikin masu raunuka sukai masa koken rashin ingancin bidigoginsu.

(3). A shekarar 1947 ne Mikhail Kalashnikov ya samu nasarar kera bindigar kuma ya sanya mata sunansa, Kalashnikov wato AK-47 Ma’ana, Automat Kalashnikov 1947.

(4). bindigar Kalashnikov (AK-47) ta kasance bindiga mafi juriya kuma mafi saukin sarrafawa a tsakankanin bindigogi.

(5). An sanya bindigar Kalashnikov a kundin-ajiya na duniya a matsayin bindiga mafi yaduwa da a kalla Miliyan dari.

(6). An yi ittifakin bindigar Kalashnikov, ta zarce hare-haren tankokin yaki, jiragen sama da rokoki kashe mutane. A kalla duk shekara, mutum 200,000 ne ke mutuwa sakamakon harsashin wannan bindiga.

(7). Baya ga samar da bindigar da kasar Rasha ke yi, har ma ta ba da lasisi ga wasu kasashe na kera bindigar. Wasu daga cikin kasashen sun hada da; Sin, Isra’ila, Indiya, Misira da Nijeriya.

(8). Akwai hoton wannan bindiga a tutar kasar Muzambique.
(9). Iyaye da dama ne a wasu kasashen Afirka suka sanya wa ‘ya’yansu maza suna ‘Kalash’ kuma saboda sunan wannan bindiga ne.

(10). A yayin da Sojojin Amurka suka kama Saddam Hussein, sun tadda shi ne da Kalashnikov wadda aka hada da zinare.

(11). Sai dai duk da kashe-kashen rayuka da ake yi da wannan bindiga, a shekarar 2007, Mikhail Kalashnikov ya kare kansa dangane da hada wannan bindiga. Cewa ya yi, ‘shi ya kera ta ne don kare kai’ Ya ci gaba da cewa, “Ni barcina nake yi garas! ‘Yan siyasa da shuwagabanni ya kamata a tuhuma don gaza kawo karshen rigingimu”

(12). Mikhail Kalashnikov ya mutu ranar Laraba, 23 disamba, 2013.

Allah Ya kare mu daga sharrin AK-47 mai dirke mutum farat daya.

Leave a Reply