DUNIYA KUNDI: Gidan sama na farko a Najeriya, Shekaru 177 da gina shi.

0
503

Daga Haji Shehu

A yau shirin duniya kundi zai leka gida Najeriya, inda zai kawo muku kadan daga cikin tarihin gidan sama na farko a Najeriya.

An gina gidan sama na farko a Najeriya a Badagry na jihar Lagos. Kamar yadda yazo a tarihi, Reverend Henry Townsend shine ya fara wannan gini na gidan saman da ya zamo wajen yawon bude yanzu haka a jihar Lagos.

An sanya tubalin fara ginin gidan a shekarar 1842 sannan an kammala ginin a shekarar 1845, Wanda ya dauki shekaru sama da Biyu ana ginawa.

Har izuwa yanzu wannan gida yana nan kuma jama’a daga sassa daba-daban na ciki da wajen kasarnan kan ziyarci wannan gini domin bawa idon su abinci kasancewar an ginashi shekaru 177 da suka gabata ba tare da Injiniyoyin zamani ba, kuma har izuwa yanzu yana tsaye da kafafun sa a doron kasa, yayinda gine gine-ginen injiniyoyin zamani masu tinkaho da ilimi kuma ke cigaba da ruftawa akan bil’adama. Ko me ya kawo haka?

Leave a Reply