DUNIYA KUNDI: Ko Kunsan Wanda Ya Kirkiri Laulawa (KEKE)

0
189

Daga Haji Shehu

Kamar ko wacce daren lahadi, shirin Duniya kundi yakan yi linkaya cikin wasu fitattun abubuwa a duniya. Yau shirin duniya kundi zai leka kadan daga rayuwar mutumin da ya kirkiri KEKE mai feda.

Kamar yadda mafi rinjayen littatafan tarihi suka nakalto, an bayyana dankasar Faransa maisuna
Pierre Lallement a matsayin wanda ya kirkiri Keke mai Feda, wanda dan Adam yake takawa da karfin tuwo ba wanda Jaki, Doki ko mutum yake ja ba.

An haifi Pierre Lallement a shekarar 1843 a wani kauye maisuna Pont-à-Mousson kusa da Nancy, a kasar Faransa.

A shekarar 1862 Lallement ya fara nazarin yadda zai Kera Keke mai Feda bayan da yaga wani nauin Keke da Dan-Adam yake turashi da hannu. Lallement ya yi nazarin saukaka wahalar dake tattare da wancan nauin Keken ta hanyar Kirkiro Keke mai Feda, wanda Dan-Adam zai hau ya tuka da kafafunsa sabanin wancan mai kafa hudu wanda ake dakon mutane a cikinsa yayinda shi mai Keken zai ke turasu da hannun sa.

Ku biyomu Ranar Lahadi mai zuwa da dare domin sake karanta wani sabon shirin.

Leave a Reply