MARIGAYI MALAM JA’AFAR KANO YA FADI GASKIYA

0
185

Daga Datti Assalafiy

ALLAH Ya jikan Mallam Ja’afar Mahmud Adam Kano da rahama Yasa ya huta, a cikin wata lakca da yayi akan Boko Haram yake cewa; “babbar matsalarmu mu Musulmai itace musulmai ‘yan boko, ‘yan Boko da sukayi karatun boko shekara talatin da ya wuce basu da tarbiyyar addini, don haka dasu ake hada kai ake cutar damu..”.

A nan Mallam Ja’afar yana magana ne akan wadannan SHAKIYYAN wadanda ake kira ko kuma masu kiran kansu da suna ‘yan Boko Aqeeda, su ‘yan Boko aqeeda sune suka salwantar ko sallamar da rayuwarsu ga Yahudu da Nasara, inda basu da wata alkibla idan ba wanda manya ‘yan Boko duniya irinsu “KARL MARX” suka dorasu a kai ba.

Ana samun irin wadannan mutane ‘yan boko aqeedah a cikin musulmai, sai dai kash, shi kanshi addinin musuluncin suna dauka ko kallonsa a matsayin kauyanci ko kuma gidadanci ko kuma wani tsohon yayi (outdated) ma’ana tsohon addini da bai dace da wannan zamanin ba.

Mafi yawan ‘yan boko aqeeda basu yarda da samuwa ko kasancewar Allah (T) ba, domin a irinsu ne ake samun “Atheist” sune “modernist”, “humanist” da dai sauran shakiyai kala-kala, hatta abubuwan rashin jin dadi da suke faruwa ga musulman duniya da nan gida Nigeria na rashin jin dadi; ‘dan Boko Aqeeda gani yake laifin Musulmai ne, saboda sunki yarda da subi zamani, sunki yarda su waye, a fahimtarsu.

A jihar Kano, akwai wani matashi dan musulmi gaba da baya da yaje yayi karatun Boko a turai, da ya dawo sai yace ya bar Musulunci, yace ba Allah, kuma ‘yan Boko Aqeeda suna nan suna goya masa baya, suna mu’amala dashi, suna jin dadin duk irin rubutun da yakeyi a wannan kafa ta social media.

Kai hatta matsalolin matsalolin da muke fama dasu a kasarnan tamu Nigeria na cin hanci da rashawa ‘yan Boko Aqida ne suka jawo mana, saboda basa tsoron Allah, ba su yarda Allah zai kashesu ya tayar dasu don yin hisabi ba, sune sukayi anfani da karatun da sukayi na Boko suka shiga cikin gwamnati, sukayi kane-kane, suka dunga tafka uwar sata, suke satar dukiyar kasa, suka bar talakawa cikin mummunan hali na rashin more rayuwa wanda talaka zai anfana, hakanne ya haifar da duk wasu kungiyoyi na ta’addanci irinsu Boko Haram da barayin shanu, da masu satar mutane da sauransu.

‘Yan boko aqeeda sunyi hakane saboda Malamansu irinsu Karl Marx sun fada musu cewa addini karyane, babu Allah, babu lahira dan haka suyi ta sata babu wanda zai tuhumesu bayan sun bar duniya.

Wadannan kadan kenan daga sharrin mutanen banza ‘yan Boko Aqeeda.

Ya kamata mu fara wani campaign wanda zamuyi amfani da alkalamin rubutu mu fahimtar da jama’armu sharri da hatsarin ‘yan boko aqeeda, ta yanda za’a wayi gari an dena zabar duk wani ‘dan boko aqeeda yayi shugabanci daga yankin mu na arewa, ba zaku taba tsammanin samun adalci daga gurin wanda bai yarda da akwai Allah ba, don haka mu gujesu, mu dena kulla kowace irin mu’amala dasu, sannan uwa uba mu dena zabansu a matsayin wakilai ko shugabanni har sai sun tuba sun yarda da Allah Madaukakin Sarki.

Muna rokon Allah Ya shafe tasirin mutanen banza ‘yan boko aqeedah, sannan Ya tsare al’ummar musulmi daga sharri da gubar da suke fesawa Amin.

Leave a Reply