DUNIYA KUNDI: Abun Al’ajabi, Rodi ya huda kansa bai mutu ba.

0
61

Daga Haji Shehu

Jaridar Daily Mail, ta nakalto labarin matashi Sanjay Bahe wanda ya gamu da mummunar tsautsayi mai cike da ban mamaki sakamakon rayuwar sa a halin yanzu. Matshin mai shekaru 21 ya fada rami a wajen da yake kwadago inda Rodi ya huda kansa daga barayin hagu ya bullo zuwa ta barayin dama.

Kasantuwar irin wannan rauni kan haddasa rasa rayi, a wannan karo abun yazo da mamaki ganin yadda murjejen rodin ya huda kan matashin kuma matashin ya cigaba da rayuwa a doron Duniya ba tare da ya samu kaduwar hankali ba.

Bayan faruwar lamarin an dauki Sanjay Bahe zuwa Asibtin B.J. dake kusa da garin Gondia a kasar Indiya, inda likitoti suka cire rodin tare da bashi kulawar farko. Likitoti sunyi matukar mamakin yadda matashin ya rayu biyo bayan daukar hoton kansa da sukayi wanda ya nuna rodin ya fasa kashin kansa ta gefen kunne sannan ya fito ta barayin kashin goshi, kuma duk da haka raunin baiyi tsananin da ya fidda shi daga hayyacin shi ba.

A cikin mintuna 90 tawagar likitoti karkashin jagorancin Dakta Pramo Giri, sukayi nasarar cirewa Bahe rodin, A karshe Sanjay Bahe ya rayu, sannan kwakwalwar sa ba ta samu matsala ba. Nan take aka dauki Sanjay Bahe zuwa Asibtin kwakwalwa domin cigaba da bashi kulawa ta musamman.

Hausawa suka ce, zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.

Leave a Reply