DUNIYA KUNDI: Riyar da tafi kowacce Rijiya tsufa a Najeriya.

0
227

Daga Haji Shehu

Shirin duniya kundi zai leka gida Najeriya inda zamu tsakuro muku kadan daga cikin tarihin Rijiyar da aka fara hakawa a Najeriya.

Rijiyar wacce take Badagry na jihar Lagos ita ce Rijiyar farko da aka fara hakawa a Najeriya, an haka Rijiyar ce domin shayarda bayi a wani wajen cinikayyar Bayi a lokacin turawan mulkin mallaka.

Tarihi ya nuna cewar Bayi ne suka haka rijiyar da kansu, kuma an haka rijiyar ne domin kaucewa guduwar bayin a lokacin da ake kaisu wajen shan Ruwa. Kafun haka rijiyar akan dauki bayin ne zuwa wani waje domin shayar dasu Ruwa, inda hakan yake bawa wasu bayin damar waskewa a hanyar zuwa shan Ruwan.

A shekarar 1840 aka gina wajen cinikayyar bayin, bayan gina wajen da shekaru 7 aka haka rijiyar, a takaicen takaitawa dai an haka rijiyar a shekarar 1847 domin shayar da bayin dake kasuwar.

Mu tara daku a ranar Lahadi mai zuwa domin kawo muku wani sabon shirin na Duniya Kundi.

Leave a Reply