BUHARIN BORNO YA TARO FADA MAI ZAFI – DATTI ASSALAFIY

0
105

Daga Datti Assalafiy

Maigirma gwamnan jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum ya nuna yatsa wa kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba “Non Governmental Organisations” (NGOs) da suke aikin bada agaji a fadin jihar Borno, yace dole su gabatar da ayyukansu karkashin kulawar gwamnatin jihar Borno imba haka ba su fice daga jihar.

Jama’a kun san dalilin da yasa Maigirma gwamna ya gindaya musu wannan ka’idar? dalilin shine su wadannan kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba, wanda nake cewa kungiyoyin sharri suna cin amanar tsaron Nigeria ta hanyar tallafawa ayyukan ta’addancin Boko Haram ta bayan fage, tare kuma da baiwa ‘yan ta’addan mafaka da yin jinya na magani garesu ‘yan ta’addan.

Mutanene suka zama annabo ‘yan ta’adda, suka gudu daga gari sukaje suka buya a jeji, aikinsu kenan kashe mutane, sai aka samu wasu kungiyoyin sharri sukazo suka mamaye muku gari, suna bin mutanen can dake kashe ku cikin jeji suna basu agaji ta bayan fage, don girman Allah wace kasa ce a duniya zata yarda da wannan cin amanar?

Idan ba’a manta ba, watannin baya rundinar Sojin Nigeria OPERATION LAFIYA DOLE sai da ta kama daya daga cikin wadannan kungiyoyin sharri da suka mamaye jihar Borno da hannu dumu-dumu suna tallafawa ‘yan ta’adda, rundinar sojin ba ta yi kasa a gwiwa ba ta dakatar da kungiyar, amma ba’a samu kwana guda ba da dakatarwan aka tilasta rundinar sojin ta janye dakatarwan da ta yiwa kungiyar, saboda yadda sukayi karfi.

Har ila yau, a shekaran da ta gabata ne, Maigirma Ministan tsaron Nigeria Malam Mansur Dan Ali ya fito ya sanarwa duniya cewa kungiyoyin bada agaji wanda ba na gwamnati ba (NGOs) da suka mamaye jihar Borno suna taimakon ‘yan ta’adda, kuma sun mayar da ta’addancin hanyar neman kudi, basa kaunar a kawo karshen ayyukan ta’addanci saboda kudin da suke samu, ku ziyarci BBC Hausa zaku samu bayanin.

Don Allah duk wanda bai san ayyukan sirri na wadannan kungiyoyin sharri ba, ya ziyarci shafina na Facebook mai sunan “Ajalin ‘Yan Boko Haram”, akwai wani rubutu da nayi a shekarar 2017 mai taken BAMU YARDA DA AYYUKAN KUNGIYOYIN DA BA NA GWAMNATI BA A JIHAR BORNO MUNAFUKAI NE, dogon rubutu ne, a rubutun na fallasa dukkan ayyukan sirri na kungiyoyin da yanda suke taimakon ‘yan ta’adda tare da basu mafaka, rubutun yana daga cikin dalilan da yasa akaci amanata aka min sharri a wannan shekarar, kuje ku duba.

Mun dauki lokaci mai tsawo muna kira da a saka ido akan ayyukan NGOs da suka mamaye jihar Borno, indai gwamnati tana son kawo karshen Boko Haram to dole gwamnati ta san ta inda kungiyoyin da ba na gwamnati ba suke samun kudi, gwamnati ta san da zamansu da rijistansu, ta san dukkan ayyukansu na sirri (secret operation), sannan gwamnati ta karanci tsare tsaren ayyukansu (mode of operation), a san inda suke zuwa da dawowa a fadin jihar Borno, a dinga monitoring dukkan motsinsu da wadanda suke bawa agaji.

Wannan shine ka’idojin da maigirma gwamnan jihar Borno yake so ya gindaya musu, aiki ne mai wahala da kuma hatsari, jama’a dole a taimakawa gwamnan Borno da addu’ah bisa wannan kyakkyawan kuduri nasa akan maciya amana kungiyoyin sharri, a abinda muka sani game da kungiyoyin babu wanda ya taba nuna musu yatsa ya wanye lafiya, balle kuma ya tona musu asiri, kamar kungiyoyin asiri haka suke, idan suka dauke ka aiki har ka fara sanin ayyukansu na sirri baka isa ka fita ba, idan sun fahimci kana shirin fita zasu kawar da kai daga duniya.

Don haka Buharin Borno na bukatar addu’ah sosai, ya taro fada mai zafin gaske da wadanda suke taimakon ‘yan ta’adda, idan yaci nasara akan wadannan kungiyoyin sharri to an samu bakin zaren da za’a warware kullin ayyukan Boko haram a yakesu a kuma kawo karshen ta’addancinsu da ikon Allah.

Yaa Allah muna tawassuli da sunayenKa kyawawa AL-HAYYU AL-QAYYUMU Ka kare mana gwamnan jihar Borno, Ka taimakeshi akan kyawawanmanufofinsa, Ka karfafi zuciyarshi akan gaskiya, Ka bashi nasara akan kungiyoyinta’addanci da masu taimakonsu Amin.

Leave a Reply