YUNKURIN BUNKASA HARKOKIN LAFIYA A JIHAR KANO:

0
60

SHARHI: Bashir Abdullahi El-bash:-

Kamar yadda aka saba, a safiyar wannan rana ta Lahadi, al’ummar Jihar Kano sun wayi gari cikin shauki da farin ciki da murna biyo bayan wani labari mai dadi da su ka samu cewa mai girma Gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje (Khadimul Islam, kuma Khadimul Umma) zai gina wasu katafarorin Asibitoci na zamani a masarautun: Gaya da Bichi da Rano da kuma Karaye. Kuma kowacce Asibiti daya za a zuba mata gadajen kwantar da marasa lafiya guda dari hudu. (400).

Me girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana haka ne yau a fadar Sarkin Rano, Alhaji, Dakta Tafida Abubakar (Autan Bawo), inda ya je domin yi wa Sarkin ta’aziyyar rasuwar dansa.

Ba kuma ga iya wannan me girma gwamna ya tsaya ba, ya kuma kara da alkawarin cigaba da inganta harkokin lafiya da ilimi da walwalar al’umma.

Kamar yadda jama’a su ka sani, Jihar Kano, Jiha ce mai dumbin yawan al’umma, kenan wannan kuduri na mai girma gwamna na sake samar da karin Asibitoci zai taimaka matuka wajen rage cinkoson marasa lafiya a Asibitocin da ake da su.

Sannan kuma, samar da karin Asibitocin zai taimaka wajen rage yawan mutuwar mata masu juna biyu musamman a yankunan karkara duba da cewar za a rage tazarar da ke tsakanin Asibitoci da al’umma.

Haka zalika, hakan zai taimaka wajen rage hasarar rayuka da ake yawan samu a sanadiyar hadarurruka da ke faruwa cikin dare da rana duba da cewar yawan Asibitocin kula da marasa lafiyar zai karu.

Baya da haka, dumbin al’ummar Jihar Kano da su ka yi karatun lafiya kuma ba sa aiki, yanzu za su samu aiki kasancewar duk wani Asibiti da za ayi sai kuma an samar masa da jami’ai (Likitoci) domin kulawa da lafiyar al’umma.

Baya ga Likitoci kuma, dubban al’umma ne za su samu ayyukan gadi da kulawa da tsaftar Asibitocin da masu goge-goge da aike-aike.

Al’ummar yankunan karkara da su ke yin tafiya me nisa kafin su samu ganin Likita, sai gashi yanzu a gwamnatin Dakta Ganduje kakarsu za ta yanke saka domin Asibitoci za su kai har inda su ke.

Ko shakka babu, al’ummar Jihar Kano ba su da da-na-sani kan gwamnatin Baba Ganduje cikin (#NextLevel). Kuma wannan abin a yaba ne matuka duba da kasancewar akasarin Gwamnoni idan sun samu damar tazarce ba su cika yin ayyuka kirki ba, amma kuma shi Dakta Abdullahi Umar Ganduje a kullum cikin ƙirƙiro da sabbin ayyuka ya ke domin kyautata rayuwar al’ummar Jihar Kano.

Baba Ganduje Kanawa mu na godiya.

Leave a Reply