DUNIYA KUNDI: Makarantar Firamare Ta Farko A Najeriya.

0
120

Daga Haji Shehu

A yau shirin duniya kundi zai tsakuro muku kadan daga tarihin makarantar Firamare ta farko a Najeriya.

…. A wacce Jiha take, a wacce shekarar aka assasata, sannan waye ya assasata?

Badagry wata unguwa ce mai tattare da tarihi, tana kusa da bakin tekun jihar Lagos inda tayi iyaka da kasar Benin ta iyakar Seme.

A lokacin turawan mulkin mallaka, turawa masu bisharar addinin kirasta sun assasa makarantar Firamare a wannan waje a shekarar 1843, a gefe kuma Badagry ta kasance wajen cinikayyar Bayi tare da lodin bayi daga wata kasa zuwa wata kasa.

A shekarar 1845, an sanyawa makarantar suna ‘St. Thomas Anglican Nursery and Primary School’ shigowar turawan mulkin mallaka tare da fara assasa makarantu a yankunan Yarabawa na daga cikin abunda ya sanya Yarabawa sukayiwa kowacce yare zarra a fagen ilimin Boko a Najeriya.

Ku biyomu ranar Lahadi da dare cikin shirin DUNIYA KUNDI Domin karanta wani sabon shirin.

Leave a Reply