LOKUTAN DA ALJANU KE SHIGA JIKIN DAN ADAM

0
126

Bismillahir-Rahmanir-Rahim.

Manzon Allah (Tsira da aminci su tabbata a gare shi) yana cewa: “Hakika shaidan (wato aljani), yana gudana a cikin jikin dan adam kamar yadda jini ke gudana”.

Da wannan ne zamu fahimci cewa; aljani kan shiga jikin dan adam, ya yi duk abinda yake so a jikinsa da yardar Allah, kuma aljanin zai iya dakatar da gudanar jini ko aikin wata gaba, ko kuma ya sanya wata cuta duk a cikin jikin dan adam, amma hakan ba zata kasance ba sai da iznin Allah (Madaukakin Sarki), domin Allah shi yake jarrabar bawa ta hanyar wani abu (wato sabab a larabce).

Malamai sun tabbatar da wadansu lokutan da aljanu ke samun damar shiga jikin dan adam, su ne kamar haka:

1. Yayin da mutum yake cikin tsananin bakin ciki ko fushi.
2. Yayin sabon Ubangiji, kamar; kallon hotunan batsa, giya ko caca da sauransu.
3. Yayin da mutum yake cikin janaba, wannan ita ce; hanya mafi yawa da aljanu ke shiga jikin ‘yan adam.
4. Yayin da mutum ya firgita ko ya razana.
Wadannan su ne hanyoyin da Malamai suka ambata.

Muna godiya ga Allah (S.W.T) da Ya bamu rai da lafiya. Kuma Muna rokon Allah (Madaukakin Sarki) Ya bamu cikakkar kariya da tsari daga sharrin aljanu/iskokai da ma mutane bakidaya.

Daga: Abdurrahman Abubakar Sada

Leave a Reply