SHUGABAN MA’AIKATANA MUTUM NE MAI GASKIYA WANDA YA FITO DAGA BABBAN GIDA” -GWAMNA GANDUJE:

0
76

DAGA: Bashir Abdullahi El-bash:-

Yau Litinin, 26 ga watan Ogusta, 2019.
A ya yin da ya karɓi baƙuncin tawagar gidansu shugaban ma’aikatansa, Alhaji Ali Haruna Makoɗa ƙarƙashin jagorancin babansa, (Alhaji Bukar Makoɗa), gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya bayyana shugaban ma’aikatan nasa a matsayin mutum mai gaskiya ɗan babban gida.

Iyalan sun ziyarci mai girma gwamna ne a wannan rana ta Lahadi, a gidan gwamnati domin yi masa godiya da bayyana masa ɗumbin farin cikinsu dangane da zaɓo ɗansu da ya yi ya ba shi matsayi mai girma a cikin gwamnatinsa.

Da ya ke jawabi a madadin iyalin, Alhaji, Alin Bukar Maƙoda, ya bayyana cewa: “Mai girma gwamna mu na matuƙar godiya da wannan karamci, mu na kuma shaida maka ba ka yi zaɓen tumun dare ba, ka yi zaɓin da ya dace. Kuma mu na ba ka tabbacin da yardar Allah ɗanmu ba zai ba ka kunya ba, zai yi aiki cikin gaskiya da amana da jajircewa kamar yadda hakan ke ƙunshe cikin tarihinsa na aiki”. Inji Alin Bukar.

Daga ƙarshe kuma ya ƙara da bayyana godiyarsu da farin cikinsu bisa wannan karamci da mai girma gwamna ya yi musu.

Da ya ke maida jawabi, gwamna Ganduje ya bayyana cewa: “Tun sama da shekaru talatin da su ka gabata, zamanin ina kan matsayin kwamishinan ayyuka, sufuri da gidaje, a lokacin gwamnatin mulkin soja ta Koloniyal Muhammad Abdullahi Wase, na riga na san Alhaji Ali Makoɗa ta ɗalilin mahaifinsa (Alhaji Bukar Makoɗa)”. Inji gwamna Ganduje.

Gwamna Ganduje ya ƙara da cewa a wannan lokaci da ya gabata, (Alhaji Bukar Makoɗa), mahaifin shugaban ma’aikatan nasa, (Alhaji Ali Makoɗa), shi ne ya yi kwangilar gina masallacin cikin gidan gwamnatin Jihar Kano. Wanda kuma a dalilin ingantaccen aiki da ya yi ga shi har yau masallacin na tsaye da ƙwarinsa.

Daga ƙarshe kuma, gwamna Ganduje ya shaida musu cewar ba su ne da godiya ba, shi ne da godiya duba da yadda su ka amince ɗansu ya karbi muƙamin da ya ba shi.

“Sannan kuma ina gode masa da ya yarda ya karɓi wannan matsayi da na ba shi, gaba ɗaya ina matuƙar godiya a gare ku”. Inji gwamna Ganduje.

Leave a Reply