A Shekarar 2017, Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, Ya Kawo Wata Ziyarar Aiki Ta Musamman Jihar Kano

0
70

WAIWAYE ADON TAFIYA JIHAR KANO A ZAMANIN GWAMNA GANDUJE (20)

TSARAWA DA GABATARWA Bashir Abdullahi El-bash

-A Shekarar 2017, Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, Ya Kawo Wata Ziyarar Aiki Ta Musamman Jihar Kano.

-Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, Ya Buɗe Wasu Manyan Ayyukan Raya Jiha Da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje Ya Yi A Cikin Ƙasa Da Shekaru Biyun.

-Ministan Lafiya Na Nageriya, Ya Yaba Tare Da Jinjinawa Gwamna Ganduje Kan Samar Da Kayayyakin Jinya Na Zamani A Asibitocin Jihar Kano.

Yau Laraba, 18 ga watan Satumba, 2019.
A cigaba da waiwayen baya kan muhimman batutuwan da su ka faru masu alaƙa da gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin gwamna Abdullahi Umar Ganduje, cikin ikon Allah yau mu na kashi na (20) daidai.

Kuma a shirin na yau, waiwayen nawa zai yi duba ne kan wata ziyarar aiki ta musamman da mai girma shugaban ƙasar Nageriya, Mallam Muhammadu Buhari ya kawo Jihar Kano a shekarar (2017), inda ya gani gami kuma da buɗe wasu ayyukan raya ƙasa da mai girma gwamna ya aiwatar a cikin ƙasa da shekaru biyun zangon mulkinsa na farko.

Kamar yadda aka sani, Jihar Kano dai Jiha ce ta masoyan shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari tun bayan shigarsa harkokin siyasa a shekarar (2003), Kano da Kanawa ba su taɓa juya masa baya ba.

Sannan kuma, mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba shi da wani abun alfahari da ya wuci shugaba Muhammadu Buhari, masoyinsa ne na gasken-ganske, wannan ƙauna da soyayya da mai girma gwamna ya ke yi ga mai girma shugaban Buhari, ita ce ma ta sanya zai yi wuya mai girma gwamna ya je wani taro ba tare da ya yi wani jawabi na yabo da fatan alkhairi ga shugaba Buhari ba.

Sai dai kuma, tun bayan samun nasarar shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da jam’iyyar (APC) a duk ƙasa a shekarar (2015), shugaban ƙasa bai samu damar ziyartar Jihar Kano ba har kusan tsawon shekaru (2) a kan madafun iko. Wanda kuma hakan ne ya ba wa maƙiya da ƴan adawa damar furta kalamai na nuna aibatawa ga mai girma girmnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Ana cikin tsaka da wannan hali ne kuma, sai ga shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari ya ba wa maraɗa kunya, inda ya kawo ziyarar aiki har ta tsawon yini (3) a birnin Kanon Dabo, tare da ziyarar gani da ido kan ɗumbin ayyukan raya jiha da mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya ke aiwatarwa gami kuma da buɗe waɗanda ya kammala, tare da dasa harsashin tubalin ginin wasu.

Bugu da ƙari, mai girma shugaban ƙasa, ya kuma gana gami da tattaunawa da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar Kano, waɗanda su ka haɗar da; ƴan siyasa, sarakunan gargajiya, malaman addini, ƴan ƙungiyoyi da kuma ƴan kasuwa.

Kamar yadda mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya faɗa, “mai girma shugaban ƙasa, Mallam Muhammadu Buhari, al’ummar Jihar Kano, har yau har gobe su na tare da kai, kuma za ka yi mamakin irin taryar da za su yi maka, domin sun shirya tsaf! Su na dakon su ga masoyinsu abin ƙaunarsu, (shugaba Muhammadu Buhari). Sannan ina ƙara tabbatar maka, a gwamnatin jiha, mun shimfiɗa ɗumbin ayyukan gina jiha da kyautata rayuwar al’umma, za ka gani kuma za ka ƙaddamar da su”.

Sauƙwar shugaba Muhammadu Buhari kuwa ke da wuya a jihar kano, ya tabbatar da maganganun da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya faɗa masa, inda ya ga dandazon taron al’ummar Kanawa su na sowa da lale marhabin da zuwan shugaba Muhammadu Buhari, inda su ke faɗin:

“Maraba! Maraba! Maraba! Sai Buhari! Sai Buhari! Sai Buhari! Sa Mai Gaskiya! Sai Mai Gaskiya! Sai Mai Gaskiya! Sai Baba! Sai Baba! Sai Baba”.

Wannan ziyara da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo Jihar Kano, ta zama wata ƴar manuniyar da ke ƙara shaidawa Duniya cewar Jihar Kano ta Ganduje ce da Buhari. Kuma ta zama silar hana maƙiya da ƴan adawar Baba Ganduje bacci a wannan rana, domin ta tabbata babu wani saɓani ko matsala a tsakanin Baba Buhari da Baba Ganduje.

Daga cikin bayanan da aka gabatarwa mai girma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, kafin azo kan ɗumbin ayyukan raya jiha, an yi masa bayani kan yadda gwamna Ganduje ya tunkari matsalar biyan albashi gadan-gadan. Inda ba daɗewa da rantsar da shi ya fidda zunzurutun kuɗi kimanin (Naira Biliyan 10) wajen biyan albashin ma’aikatan da su ke bin gwamnatin baya bashin albashi na waɗansu watanni da su ka gabata.

Da aka dawo fannin ayyukan raya jiha kuwa, shugaban ƙasa Buhari, ya buɗe wasu manyan aaibitoci guda biyu, waɗanda mai girma gwwmnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya gada ya kuma kammala. Sannan gwamna Ganduje ya samar da dukkan tsarin kula da kiwon lafiya mai nagarta da inganci a asibitocin ta yadda hakan zai ba wa al’umma marasa hali damar samun tsarin kiwon lafiya mai nagarta.

Wannan kuma, shi ya ƙara fito da nagartar mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan yadda ba ya watsi da duk wani aiki da ya gada daga gwamnatocin baya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya fidda zunzurutun kuɗi kimanin (Naira Miliyan 964,883,036.56) da kuma (Naira Miliyan (1,999,053,126.54) domin zuba gajdajen kwanciyar marar lafiya irin na zamani a asibitocin biyu, na hanyar zuwa gidan Zoo an sanya gadaje guda (250), ya yin da shi ma asibitin na Giginyu aka zuba gidaje kimanin guda (250).

A ya yin da Ministan Lafiya ya ga irin ɗumbin kayan zamani da mai girma gwamna, Dakta Ganduje ya zuba a asibitocin, shi da kansa sai da ya jinjina masa tare da faɗin cewar ba shakka mai girma gwamna ya yi namijin ƙoƙari matuƙa.

Wani aikin kuma da mai girma shugaban ƙasa, Muhamadu Buhari ya buɗe, sun haɗa da aikin hanyar Madobi zuwa Panshekara, da kuma titin yankunan (CBN), aikin da mai girma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kashe masa Biliyoyin naira domin rage cunkoson ababen hawa da kuma kyautata muhalli da harkokin sufuri.

Daga cikin ayyukan da mai girma shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ziyarta, sun haɗa har da aikin samar da kamfanin taki na Jihar Kano, wato “Kano Agricultural Supply Company” (KASCO). Kamfanin da mai girma gwamna ya samar domin wadata jihar kano da ƙasa gaba ɗaya da taki. A cigaba da ƙarfafar manufar gwamnatin shugaba buhari ta inganta harkokin noma a ƙasa gaba ɗaya.

Haka zalika, shugaba buhari ya ziyarci wasu ayyukan samar da kamfanin shinkafa da wasu ƴan kasuwa su ke yi domin ƙarfafar manufar gwamnatim shugaba buhari na wadata ƙasa da abinci. aikin da ya ke lakume bilihoyin dalolin amurka.

Sai kuma aikin samar da cibiyar koyar da matasa sana’o’in hannu daban-daban kimanin sana’o’i (22) domin samawa matasa madogara su zamto masu tsayuwa da ƙafafunsu wanda mai girma gwamna ya ke kashe mata biliyoyin nairori. Kuma tuni wannan cibiya ta kammala.

Sai kuma sabuwar katafariyar kasuwar zamani ta jihar kano, (Kano Economic City) da kuma katafariyar masana’antar sarrafa kaya ta kantin kasuwar kwari, wanda mai girma gwamna ya samar domin bunƙasa harkokin kasuwanci a Jihar Kano.

Leave a Reply