A cikin watanni biyar an yi wa mata 42 fyaɗe a jihar Kano – rahoton ƴan sanda

0
508

Rundunar ƴan sanda ta ƙasa reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta samu laifuffukan fyaɗe guda 42 daga watan Janairu zuwa watan Mayu.Kakakin rundunar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN.

 

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce binciken rundunar ƴan sanda reshen jihar Kano ya samu laifuffukan fyaɗe guda 42 a faɗin jihar Kano, wanda kawo yanzu sun gurfanar da su a gaban kotuna.

 

 

Ya ƙara da cewa fiye da kaso 33 na waɗanda aka yiwa fyaɗen an yi musu ne a cikin kwangwayen gini, a inda fiye da kaso 17 aka aikata musu fyaɗen a cikin gonaki, sai kuma kaso 15 aka yi musu a cikin shaguna, yayin da fiye kashi 8 aka yi musu fyaɗen a makarantu.

 

Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce fiye da kaso 6 kuma da aka yi musu fyaɗen a gidajensu da kuma kasuwanni aka yi musu.

 

Hakazalika kakakin rundunar ƴan sandan ya ƙara da cewa jami’an ƴan sanda za su cigaba da sanya ƙafar wando da duk wanda su ka samu da aikata wannan mummunar ɗabi’ar ta fyade.

 

A ƙarshe DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an samu ragowar aikata fyade a jihar Kano idan aka kwatanta da waccan shekarar, ya kuma buƙaci al’umma da su cigaba da kawo rahoton waɗanda su ke aikata fyade, domin hakan ne zai ƙara daƙile wannan ɗabi’ar.

 

 

 

 

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here