A Gobe Likitocin Nijeriya Za Su Janye Yajin Aiki

0
192

Rahotanni sun tabbbatard a cewa; kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta Nijeriya ta sanar da janye yajin aikin da membobinta suka tsunduma daga gobe Litinin 22 ga watan Yuni biyo bayan ganawar uwar kungiyar da gwamnati kan bukatun da suka tilasta musu tafiya yajin aikin gargadin.

Cikin wata sanarwar bayan taro da kungiyar ta raba mai dauke da sa hannun shugabanta na kasa Dr Aliyu Sokomba, ta ce sun dauki matakin janye yajin aikin ne don baiwa gwamnatocin jihohi da tarayyar damar cika alkawuran da suka dauka.

A cewar sanarwar tun farko shugaban majalisar wakilan kasar Femi Gbajabiamila da sakataren gwamnati Boss Mustapha da kuma shugaban kungiyar gwamnonin kasar Kayode Fayemi ne suka shiga tsakanin gabanin amincewa da matakin janye yajin aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here