A jihohin Abuja da Niger ambaliyar ruwa ta yi ajalin mutane 26

0
3375

Mutane 26 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku a Abuja babban birnin tarayya da jihar Niger da ke maƙwaftaka da Abujan.

Daraktan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Niger Alhaji Ibrahim Ahmed Inga ne ya shaida cewar mutane 11 sun mutu yayinda wasu 6 suka bata sakamakon ambaliyar da ta afku a jihar.

Inga ya ce ana ci gaba da gıdanar da aiyukan neman wadanda suka bata, kuma daruruwan mutane sun rasa matsugunansu.

A yankin Gwagwalada na babban birnin tarayya Abuja kuma mutane 15 da suka hada da wata mace mai juna biyu sun mutu inda wasu 30 suka bata sakamakon ambaliyar ruwan da ta afku.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here