A karon farko bayan shekaru 70 an yi bikin saukar Alkur’ani a birnin Sophia

0
40097

A karon farko bayan shekaru 70 an sauke Alkur’ani Mai Tsarki a Sophia Babban Birnin ƙasar Bulgeriya.
Dalibai 17 ne suka gudanar da saukar a lambun da ke bayan Babban Masallacin Juma’a na Banya da ke Babban Birnin Bulgeriya.
An gudanar da taron saukar tare da wakokin Musulunci karkashin jagorancin Kungiyar Hadin Kan Addini ta Musulmai Turkawa.
Shugaban Diyanet a Sophia Dr. Mustapha Alish Haci, Shugaban Majalisar Shura ta Bulgeriya Vedat Ahmet, Shugaban Hadin Kan Addinan Bulgeriya Birali Birali da Sakataren jakadan Turkiyya a Sophia Mehmet Genc na daga cikin wadanda suka halarci taron saukar.
A karshen taron an rabawa daliban kyaututtuka masu kayatarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here