A Karon Farko Shugaba Buhari Ya Sanya Takunkumin Fuska

0
3043

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karon farko ya bayyana da takunkumin fuska tun bayan bullar annobar korona a Nijeriya a watan Maris din 2020. Shugaban ya sanya takunkumin fuskar ne a yayin da ya kai ziyara kasar Mali domin tattauna rikicin siyasa da yake aukuwa a kasar.

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban ya isa kasar ta Mali domin yin sulhu kan rikicin siyasar kasar a yau Alhamis.

Isar shugaban kasar ta ja hankali jama’a ba, sakamakon ganinsa da takunkumin rufe fuska.

Gwamnatin tarayya dai tuni dama ta wajabta sanya takunkumin rufe fuska a bainar jama’a, sai dai shugaban kasar bai taba sanya shi ba duk da yake ya sha gudanar da taruka a bainar jama’a.

Majiyarmu ta labarto cewa shugaba Buhari ya tafi Mali ne bayan tattaunawar da ya yi da tsohon Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙungiyar ECOWAS da suka je Mali domin sasanta rikicin siyasar kasar.

‘Yan adawar kasar ta Mali sun kwashe kwanaki suna gudanar da zanga-zanga, inda suke neman Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta ya sauka daga mulki saboda kasa magance rikicin ‘yan bindiga, da na tattalin arziki da kuma zaben da ake takaddama a kan sakamakonsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here