A tarihin Najeriya babu gwamnatin da ta yi nasarar yaƙi da cin hanci kamar ta Buhari – Fula

0
4376

Wakilin mazabar Kirikasamma da Guri da kuma Birniwa a majalissar wakilai ta kasa Dakta Abubakar Hassan Fulata yace babu wata gwamnati data samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan irin gwamnatin tarayya karkashin tutar jamiyyar APC.

Dr Abubakar Hassan Fulata ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da manema labarai a birnin Dutse, a jihar Jigawa.

Yace gwamnatin tarayya tana aiwatar da tsarin ba sani ba sabo wajen hukunta duk wanda aka samu da lefin cin hanci da rashawa inda yace tuni aka zartar da hukunci akan yan majalissar dokoki ta kasa da manyan shugabanni da aka samu da lefin cin hanci da rashawa a kasar nan.

Da ya juya ga bangaren tsaro kuwa, Dr Abubakar Hassan Fulata yace an samu nasarori da akasin hakan, inda yace watanni biyu da suka gabata majalisar dokoki ta kasa tayi kudirin dokar cire dukkannin manyan hafsoshin sojin kasar nan tare da maye gurabensu da wasu sabbi inda har yanzu suke jiran amincewar shugaban kasa.

Yace majalissar ta kafa karamin kwamiti domin bincikar yawan adadin gudunmawar kudade da Nigeria ta samu daga cutar corona da nufin sanin yadda aka yi amfani dasu.

Akan batun aiyukan mazabu kuwa, Dr Abubakar Hassan Fulata yace cutar corona ta kawo cikas wajen aiwatar da aiyukan mazabu a bana sakamakon faduwar darajar man fetir.

Yace gwamnatin tarayya ta bada basuka da kuma tallafi ga manoma domin rage radadin cutar corona a fadi n kasar nan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here