Abdulateef Suleiman Mataimaki Na Musamman Ga Gwamna Bello Ya Rasu

0
215

Rahotonnni na nuni da cewa; Malam Abdulateef Suleiman, mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya rasu sakamakon rashin lafiya da ya yi fama da ita.

Malam Muhammed Onogwu Sakataren yada labaran gwamnan Kogi shi ne ya bayyana sanarwar rasuwar Abdulateef Suleiman, inda ya tabbatar da cewa ya rasu ne a yau Laraba.

Malam Suleiman ya rasu ne a wani asibiti mai zaman kansa dake birnin tarayya Abuja sakamakon ciwon da ya shafi zuciya.

Za a yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a yau Laraba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here