Abin Damu Wa Ne Yadda Mutane Ba Su Yadda Da Korona Ba –Kwamishinan Lafiya

0
161
Coronavirus economic impact concept image

Kwamishinan lafiya na jihar Abiya, Dr Joe Osuji, ya bayyana cewa matsalar da ake fuskanta a yaki da cutar Korona a jihar shi ne, mafi yawan al’umma a jihar ba su yadda da cutar ba.

Osuji ya bayyana hakan ne a garin Umuahia a ranar Juma’a a yayin ganawa da ‘yan jarida.

Kwamishinan ya bayyana damuwarsa bisa yadda al’umma suka yadda cewa gwamnatin jiha na amfani da cutar ne wajen neman kudi daga gwamnatin tarayya da kuma masu bada tallafi.

Sai dai ya ce hakan ba gaskiya bane, domin cutar tabbas ko gaskiya ce, kuma cutar ta zo ne domin ta zauna. A don haka ya nemi al’umma da bi matakan kare kansu daga cutar.

Ya nuna yadda sakamakon sanya na’urar gwajin cutar a jihar, zuwa yanzu an gwada mutane da dama. Inda kuma ya bada tabbacin sake sanya wadansu na’urorin a makonni masu zuwa domin fadada gwajin masu cutar.

An sanya na’urar gwajin cutar ne a Babban Asibiti dake Amarachara,  wanda asibitin ya zama daya daga cikin cibiyoyin gwajin cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here