Afrika Ta Kudu: Kotu ta dakatar da sammacin kama Jacob Zuma

0
164

Babbar kotun a kasar Afrika ta Kudu ta soke sammacin kama tsohon shugaban kasar, Jacob Zuma bayan da lauyoyinsa suka mika wa kotun takardar shaidar rashin lafiyarsa.

A cikin wata Fabarairu ne kotu ta bada sammacin kama Mr Zuma bayan ya ki bayyana a gabanta.

Jaridar BBC Hausa ta rawaito cewa, Lauyoyinsa sun ce tsohon shugaban kasar a wancan lokacin yayi balaguro zuwa kasar Cuba domin karbar magani.

A yau aka ci gaba da sauraron karar a shari’ar da ake masa bisa zargin ya karbi cin hanci a wajen wani kamfanin kasar Faransa shekaru 20.

An dage sauraron kasar zuwa watan Satumba.

Hukumomi a Jamhuriyar Dimokoradiyyar Congo na kara nuna fargaba kan yadda iyaye ke aike wa da yaransu wajen hakar ma’adanai na Lualaba da ke kudu maso gabashin kasar duk kuwa da hadarin da wajen ke da shi, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

An samu raguwar bukatar karfe a duniya kamar su Cobalt sakamakon annobar korona, wanda hakan ya janyo raguwar abin da masu hakar ke samu, in ji Reuters.

Ya kara da cewa fitar da nau’in karfe na cobalt ya ragu da kashi 15.2 cikin 100 a watanni ukun farko wannan shekarar idan aka kwatanta da yadda yake a irin lokacin a bara.

Fargabar da ake da ita ce idon iyayen ba sa samun kudin da zai ishe su bukatunsu na yau da gobe, za su rika fitar da yaransu daga makaranta suna mai da su ayyukan hakar ma’adanai masu cike da hadari.

“Tattalin arziki ya fuskanci mumunan koma baya yayin wannan matsalar lafiyar da aka samu, wanda hakan zai shafi abin da iyayen ke samu.. sai dai bai kamata wannan ya zama dalilin amfani da yara wajen aikin hakar ma’adanai ba,” in ji wani jami’i da ke lura da harkokin tattalin arzikin yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here