Aisha Buhari ta bi sahun masu zanga-zangar kan rashin tsaro a Arewacin Najeriya

0
122

 

Mai dakin shugaban ƙasa Aisha Buhari ta bi sahun masu kira a kawo karshen rashin tsaron da ke addabar Arewacin Najeriya.

Matar shugaban kasar ta wallafa wani sako a shafinta na Twitter ranar Asabar tare da wakar mawakin Kannywood Adam A. Zango inda yake kokawa kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin Najeriya.

Sakon nata na dauke da maudu’in #Achechijamaa, wanda ke nufin a ceci rayuwar jama’a. Wakar na dauke da hotunan shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da manyan hafsoshin tsaron kasar da ke nuna su a fadar shugaban kasa suna ganawa.

Wasu daga cikin baitukan wakar na cewa:

“Don Allah a duba,

Taimakonka [Shugaba Buhari] muke nema

Arewa na kukaye,

Ana zubar da jininmu

Ana kashe al’umarmu

Ana ta zubar da jininmu…

Masu amshin suna kiran sunan Baba, wato Shugaba Buhari.

Mai dakin shugaban kasar ta wallafa sakon ne a yayin da ‘yan Najeriya, musamman daga kudancin kasar ke tsaka da zana-zanga kan gallazawar da rundunar ‘yan sandan kasar da ke yaki da fashi da makami ta SARS take yi musu.

Suna amfani da maudu’in #EndSars don jawo hankali kan wannan matsala da ma wasu matsalolin da ke addabarsu.

Kazalika takwarorinsu na arewacin kasar suna tasu zanga-zangar kan tabarbarewar tsaro a yankin inda suke amfani da mau’du’in #SecureNorth don bayyana halin da yankin ke ciki.

Daruruwan mutane ne suka mutu yayin da dubbai suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a arewa maso yammacin kasar a shekarun baya bayan nan.

Hakan na faruwa ne a yayin da yankin ke ci gaba da fama da hare-haren mayakan Boko Haram wadanda aka kwashe shekara da shekaru ana fuskanta.

Mai dakin shugaban kasar ta dade tana korafe-korafe kan gwamnatin mijinta.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here