Akwai mutane sama da dubu 80 masu shekaru sama da 100 a Japan – Rahoto

0
87

A kasar Japan an gano akwai mutane sama da dubu 80 da suka haura shekaru 100 a duniya.

Ma’aikatar Lafiya, Kwadago da Walwalar Jama’a ta ƙasar Japan ta sabunta alkaluman yawan jama’ar kasar da kuma shekarunsu.

Alkaluman sun nuna cewar mutanen da suka haura shekaru 100 a duniya sun karu da dubu 9,176 inda adadinsu ya kama dubu 80,450.

A shekaru 50 da suka gabata wannan adadi ya karu sosai, kuma mata ne suke da kaso 88 cikin 100 na adadin.

Mafi yawan wadanda suka haura shekaru 100 a Japan na a jihar Shimane inda jihohin Kochi da Tottri suke biye mata baya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here