Akwai yiwuwar mu sake rufe Kaduna~El-rufa’i

0
290

Gwaman Jihar Kaduna Malam Nasir El-Erufa’i ya ce akwai yiwuwar zai sake rufe jihar matukar  jama’a suka ci gaba da saba ka’idojin kariyar cutar COVID-19.

El-Rufa’i ya bayyana haka ne yayin kaddamar da dakin gwajin COVID-19 na tafi da gidanka wadda Hukumar USAID ta ba wa jihar.

Ya ce idan aka kai matakin da yaduwar cutar ta fi ƙarfin cibiyoyin lafiyar da ma’aikatan lafiya a jihar, dole ya sake sa dokar hana fita.

“A baya mun saukaka dokar kullen ne saboda mun gamsu da tsarin gwaji da muke yi, sannan kuma da wadatattun kayan gwajin da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya.

“Don haka ina kira ga al’ummar Jihar Kaduna da su ci gaba da bin matakan kariya, su kuma guji yawan fita har sai yin haka ya zama dole.

“Idan bukatar sake kulle jihar ta taso, ba za mu yi kasa a gwiwa ba, za mu sake rufe ta. Gara mu tsare lafiyar al’ummarmu, in ya so daga baya sai mu nemi afuwarsu”, inji shi.

Nasir El-Rufa’i ya ce dakin gwajin tafi-da-gidankan a cikin babbar mota, Gwamanatin Amurka ce ta ba wa jihar ta hannun hukumar USAID domin yin gwajin cutar tarin fuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here