Al’ajabi: Zakara ya kashe wani jami’in Ɗan Sanda

0
490

Wani jami’in ɗan sanda mai suna Christian Bolok, a ƙasar Philippines ya rasa ransa a lokacin da ya je kame a wani gidan wasa da Zakaru, sakamakon harin da zakaran ya kai masa.

Tun da farko rezar da ke jikin kafar zakaran ce ta yanki dan sandan a Cinya wanda hakan yayi sanadiyyar zubar da jini sosai, bayan da aka garzaya da shi azibiti domin ceton lafiyarsa, a nan likitoci su ka tabbatar da mutuwarsa.

Wasa da Zakara a kasar Philippines wata al’adace wacce mahukuntan ƙasar su ka amince sa yin ta a lokutan hutu ko kuma wasu ranaku na musamman da babu aiki, sai dai zuwan annobar cutar Coronavirus mahunkuntan ƙasar sun haramta duk wani wasa da zai kawo cunkuson jama’a.

Kamfanin dillancin labaran kasar PNA ya bayyana cewa lamarin ya farune a ranar Litinin 26 ga watan nan a yankin arewacin Samar.

Shugaban rundunar ƴan sandan yankin ya bayyana cewa a shekaru 25 da ya yj yana aiki, bai taɓa samun irin wannan rahoto ba.

A ƙarshe rundunar ƴan sanda ta samu nasarar damƙe mutane 3 da su ka shirya wasan Zakarun, tare kuma miƙa ta’aziyya ga iyalan mama cin.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here