Alhaji Bashir Jigo A APC Ya Jinjinawa Buhari Bisa Sulhunta ‘Ya’yan Jam’iyyarsa

0
126

Alhaji Bashir Rimin -Zayam, wani babban jigo a APC a garin Bauchi ya jinjinawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa shiga tsakani kan rigimar da ta barke a cikin jam’iyyar ta APC.

Bukar ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a ranar Litinin a garin Bauchi, inda ya ce rushe majalisar zartaswa da Buhari ya yi, hanya ce ta daukar matakin gyara.

Ya tabbatar da cewa wannan matakin zai kara karfafa APC din ne domin ci gaba da gudanar da ayyukanta. Ya ce domin ba kyakkyawan abu bane a ce ana rikici a jam’iyyar da take jagorantar kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here