Al’ummar Tangaza Sun Jinjinawa Gwamna Tambuwal Bisa Ganin Sabuwar Kwalejin Ilimi Jihar Ta Fara Aiki

0
280

Al’ummar Gidan Madi dake karamar hukumar Tangaza a jihar Sakkwato, sun jinjinawa gwamna Aminu Tambuwal bisa yadda ya nuna hobbasarsa wajen ganin sabuwar Kwalejin Ilimi ta gwamnatin tarayya, FCE da aka kai yankin ta fara aiki.

Malam Sharifuddeen Sidi da Malam Bello Tangaza sune suka yi wannan jinjinar a yayi ganawa da manema labarai a ranar Litini a Sokoto.

Sidi ya bayyana ziyarar da gwamnan ya kai wurin a matsayin wani mataki na ganin Kwalejin ta fara aiki, inda Sidi ya shawarci al’ummar yankin da su yi amfani da wannan dama na makarantar wajen ci gaba da karatu.

 

Ya kuma yi kira ga mazauna yankin da su shiga makarantar domin daukar darussa daban-daban da makarantar za ta karantar.

Ya yi bayanin cewa; lallai wannan makaranta da aka kai Tangaza za ta taimaka wajen akalla mutanen yankin su samu shaidar karatu ta NCE. Wanda ya ce wannan wata matakala ce ta shiga jami’a.

Idan zaku iya tunawa, gwamna Tambuwal ya yi alkawarin bai wa makarantar gudummawa dari bisa dari a lokacin da shugaban hukumar kula da kwalejin ilimi ta kasa, NCCE, Farfesa Baffa Aliyu ya kai masa ziyara.

Gwamnan ya mika godiyarsa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa sanya wannan makaranta a yankin, inda kuma ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ba da dukkanin gudummawar da ake da bukata wajen ganin makarantar ta fara aiki.

Gwamna Tambuwal ya ce zai ga cewa Kwalejin ta fara aiki ta hanyar biyan diyya a wurin da aka zaba domin gina makarantar na wucin gadi da dindindin.

Shugaban NCCE, ya nuna gamsuwarsa bisa abubuwan da ya gani a kasa, inda ya ce yana da kwarin guiwar cewa makarantar za ta fara aiki a watan Oktoba bisa abin da idonsa ya gane masa, kamar yadda shugaban Buhari ya bada umurni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here