Al’ummar unguwar Badawa a birnin Kano sun tsinci gawar wani matashi yashe a Bola

0
244

Al’ummar unguwar Badawa da ke yankin ƙaramar hukumar Nasarawa a jihar Kano sun tsinci gawar wani matashi da aka kashe aka jefar a bola.

Shafin jaridar Kano Focus ya ruwaito cewa an tsinci gawar matashin ne a ranar Talata bayan da aka daureshi a cikin wani buhu tare da yasar da gawar a cikin bolar.

A cewar shaidun gani da ido mamacin da aka tsinta bai gaza shekaru arba’in ba

Tukur Bala mazaunin unguwar ta Badawa ya ce sun tsinci gawar ne a ranar Talata cikin wata kwata da ta gifta ta wata bola a unguwar.

Ya ce gurin an saba zubar da shara da hakan ya sa saida gawar ta fara wari a cikin buhu tukunna aka gano ta.

Malam Bala ya ce a kalla gawar mutumin za ta kai shekaru arba’in.

Ya ce wannan ba shi ne karo na farko da aka tsinci gawa a yankin ba, a cewarsa akwai bukatar daukar matakin da ya da ce domin kawo karsehen matsalar.

A nasa bangaren shugaban rundunar ‘yan Sintiri ta (vigilante) na jihar Kano Muhammad Kabir Alhaji ya ce tuni suka dauki gawar suka kuma mikawa jami’an yan sanda.

Sai dai mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce ba su samu rahoto kan al’amarin ba.

Abdullahi Kiyawa mai mukamin mataimakin sufurtandan ‘yan sanda ya ce za su bincika kuma da zarar sun samu bayani za su sanar mana.

Kano Focus

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here