Ambaliyar ruwa tayi ajalin Mutane 8 tare da rusa dubban gidaje a Katsina

0
897

Hukumar bayar da agaji gaggawa ta jihar Katsina SEMA ta tabbatar da mutuwar mutane 8 tare da rushewar gidaje fiye da 3000 a dalilin ambaliyar ruwa da aka samu a jihar.

Babban sakataren hukumar ta SEMA, Babangida Nasamu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, inda ya ƙara da cewa ambliyar ruwan kuma ta lalata kimanin kadada fiye da 7000, wanda hakan ya haifar da babbar asara ga manoma.

Babangida Nasamu wanda ya samu wakilcin jami’in yaɗa labarai na hukumar ta SEMA, ya ce baya ga rasuwar mutum 8, akwai akalla mutane 17 da su ka samu munanan raunuka.

Haka kuma Babangida Nasamu ya ce daga watan Janairun shekarar nan zuwa yau babu wata ƙaramar hukuma a cikin ƙananan hukumomi 34 da ake da su a jihar Katsina, da ba su samu rahoton ambaliyar ba.

Hakazalika babban sakataren ya ce mafi ƙarancin ɓarnar da ambaliyar ta yi shi ne na rushewar gidaje 103 a ƙaramar hukumar Kankara, yayin da aka samu adadi mafi yawa na rushewar gidaje guda 3,568 a ƙaramar hukumar Katsina.

A ƙarshe ya ce tuni hukumar sa ta SEMA tana tantance waɗanda abin ya shafa domin basu tallafin da ya dace domin rage musu  raɗaɗi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here