Amitabh Bachchan: Tauraron fina-finan India ya warke daga Covid-19

0
2714

An sallami fitaccen tauraron fina-finan India, Amitabh Bachchan, daga asibiti bayan ya warke daga Covid-19.

A watan jiya ne Mr Bachchan mai shekara 77 ya shaida wa miliyoyin masu bibiyarsa a Twitter cewa ya kamu da cutar korona.

Ranar Lahadi, ya ce ya bar asibiti bayan ya warke daga cutar.

Ya gode wa magoya bayansa bisa addu’o’in da suka yi masa, da kuma ma’aikatan asibitin Nanavati da ke Mumbai bisa “kwarewarsu” ta aiki.

An kwantar da Bachchan a asibiti a watan jiya tare da dansa Abhishek, wanda shi ma ya kamu da cutar. Kazalika surukar taurarom da jikarsa sun harbu da cutar.

A halin da ake ciki India na fama da karuwar kamu dauke da cutar korna.

Ranar Lahadi mutum fiye da 50,000 sun kamu da cutar karo na hudu a jere. Maharashtra, cibiyar kasuwancin kasar, Mumbai, na cikin wuraren da cutar ta fi kamari ko da yake ana samun karuwar masu fama da cutar a wasu jihohi kamarsu Andhra Pradesh, Telangana da kuma Assam.

A gefe guda, ranar Lahdi ministan harkokin cikin gidan India Amit Shah ya ce ya kamu da cutar korona.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mr Shah ya ce ba ya jin wata alamar rashin lafiya amma an kwantar da shi a asibiti sakamakon shawarwarin likitoci.

Amitabh Bachchan ya yi fina-finai akalla 200 a tsawon shekaru 50 da ya shafe yana fina-finai a masana’antar Bollywood.

Mista Amitabh na daya daga cikin shahararrun jaruman fim a duniya. Yana da milyoyin mabiya a Indiya, da kudancin Asiya da sauran kasashen duniya.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here