An samu ƙarin mutane miliyan 9 da ke samun ruwa mai tsafta a Najeriya – Minista

0
401

Ministan kula da albarkatun ruwa na ƙasa Suleiman Adamu, ya ce an samu ƙarin mutane miliyan tara da suke samun tsaftataccen ruwan sha.

Suleiman Adamu ya bayyana hakan ne a wurin taron nuna muhimmancin tsaftataccen ruwan sha da ya gudana a birnin tarayya Abuja, inda ya ce an samu ƙari sosai na mutanen da ke wadatuwa da tsaftataccen ruwan sha daga kashi sittin da takwas cikin ɗari a shekarar 2018 zuwa kashi saba’in cikin ɗari a shekarar da ta gabata.

Wannan dai yana zuwa a lokacin da yawanci kasashe masu tasowa ke fama da matsalar samun tsaftataccen ruwa, wanda hakan ke jefa dumbin jama’a cikin mawuyacin hali kamar kamuwa da cutuka da dai makamantansu

Rashin tsaftataccen ruwan sha a Najeriya dai wata babbar matsala ce da ta addabi birnin da kauye a kasar, inda jama’a ke ta kokawa akai.

Haka kuma masharhanta na ganin batun cimma burin samar da ruwan sha mai tsabta da kuma wadatarsa a kasashen duniya wani babban kalubale ne ga hukumomi.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here