An Sanya Ranar Da Za A Bizne Ajimobi

0
206

A ranar 28 ga watan Yuni ne za a rufe gawar tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi,. Inda za a bizne gawarsa ta shi a Babban Masallacin Sanata Ishaq Abiola Ajimobi dake garin Oke-Ado, Ibadan da misalin karfe 12 na rana.

Bolaji Tunji, Kakakin Marigayi Ajimobi din ne ya bayyana hakan a cikin takardar tsarin yadda za a bizne Marigayin wanda ya fitar a ranar Juma’a a Ibadan.

Tunji ya ce iyalin Marigayin ne suka tsara yadda za a bizne shi tare da hadin guiwar gwamnatin Legas da ta Oyo.

Iyalin mamacin sun nemi da su bi ka’idojin kariya daga cutar Korona a yayin bizne shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here