An yi min wahayi daga shugaba Buhari sai ni – Tunde Bakare

0
242

Fitaccen faston ‘Pentecostal’ a Najeriya, Tunde Bakare, ya yi ikirarin cewa zai tsaya takarar shugabancin kasa a zaben 2023, kuma shi ne zai yi nasara.

Bakare, wanda shi ne babban fasto a Cocin Letter Rain Assembly, ya bayyana wannan furuci a cikin wani bidiyo da aka rika yadawa a Facebook da Twitter.

Ya ce ubangiji ne ya ce ya tsaya, kuma idan ya tsaya, zai yi nasara. Sannan kuma shi ne zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari bayan Buhari ya kammala wa’adin sa a cikin 2023.

“Bari wanda bai ji ba, to za ni fada da babbar murya a yau cewa a yadda siyasar Najeriya ke tafiya, Shugaba Muhammadu Buhari shi ne na 15, ni ne na 16,” Haka Bakare ya furta a cikin wani bidiyo, yayin da ya ke magana a cikin cocin sa a Lagos.

Bakare, mai shekaru 64 a duniya, shi ne ya fito a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa na Buhari a zaben 2011, wanda ba su yi nasara ba.

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da mataimakin sa Namadi Sambo na PDP ne suka kayar da su.

“Idan Buhari na son tsayawa a 2019, ban damu ba. Har yanzu shi ne na 15. Sai bayan ya sauka sannan ni kuma zan hau mulki.”

Wannan furuci ya na mufin lallai ya yi wannan magana ce kafin zaben shugaban kasa a 2019.

Jin wadannan kalamai daga bakin Bakare ya sa mambobin da ke cikin cocin daga hannaye sama su na tsalle da murna da kuwwar godiya ga ubangiji, dangane da jin wannan bushara daga Bakare.

“Ai ban taba yi muku irin wannan maganar a baya ba. To amma a safiyar yau na yi muku wannan magana. Da sunan Yesu Almasihu babu abin da zai iya canja wannan alkawari.

“Daga Buhari sai ni, maganar kenan.”

Mahalarta cocin wadanda akasarin su duk a tsaye su ke, sun ci gaba da kuwwa babu kakkautawa.

Daga nan sai ya fara yanko ayoyi a cikin Bebul ya na nuna cewa Buhari ba zai iya kai Najeriya wata kololuwar da ake tunanin zai iya kai ta ba.

“To ni ne zan dora daga inda Buhari ya tsaya, kuma ni zan kai Najeriya kololuwar da ake tunanin za a iya kai ta, inda Buhari ba zai iya kai ta ba.” Inji Bakare.

 

An Wallafa wannan Labarin a shafin Premium Times a cikin watan Satumba na shekarar 2019

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here