Ana yunƙurin shigo da Kaji masu ɗauke da cutar Korona cikin Najeriya – Hukumar Kwastan

0
288

Hukumar hana fasakauri ta kasa ta yi gargadin cewa ana shirin shigo da danyun kaji daga kasar Sin da Ecuador.

A takardar umarnin, hukumar ta gargadi jami’anta su tsaurara tsaro a dukkan tashohin jiragen sama da iyakokin Najeriya.

Takardar mai dauke da kwanan watan, 9 ga Satumba, 2020,wanda mukaddashin mataimakin kwantrola, I. T Magaji ya sanyawa hannu, ya sanar da dukkan jagororin gundumomi, garuruwa da iyakoki, cewa gwamnatin kasar Sin ta samu cutar Korona cikin kayan abincin da aka shigar kasar.

Saboda haka, kwantrola janar na kwastam, Kanar Hameed Ali, ya gargadi dukkan hafsoshi su tsaurara tsaro da lura wajen tabbatar da cewa kajin nan basu shigo Najeriya ba.

Wani sashen jawabin ya ce: “Labarin leken asiri da hedkwata ta samu ya bayyana cewa yayin tantance namomi, gwamnatin kasar Sin ta gani gano fiffiken kaji da jatan lande da aka shigar daga kasar Brazil da Ecuador na dauke da cutar Korona.”

“Saboda haka ana tunatar da ku cewa shigo da kaji, matattu ko rayayyu ta iyakokin kasa ko sama ko jiragen ruwa haramun ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here