Ana zargin tsohon shugaban jam’iyyar PDP da satar na’ura mai ƙwaƙwalwa da kayan shayi

0
4839

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP reshen jihar Plateau Yakubu Chocho da wasu mutane guda 3 sun gurfana a gaban babbar kotun shari’a ta I da ke Kasuwar Nama a binin Jos, bisa zargin laifin sata da hadin baki da kuma aikata rashin gaskiya.

Yakubu Chocho ya gurfana a gaban kotun ne tare da sauran mutane uku da ake tuhumarsu tare da shi. Mutanen sune Helen Yakubu, wacce ta gudanar share-share a shalkwatar jam’iyyar, sai kuma Samka Gyol wanda ya ke shi ne maigadi da kuma Adamu Garba.

Tun da farko wasu rahotanni sun bayyana cewa Helen da Samka Gyol su na aiki ne a shalkwatar jam’iyyar PDP da ke kan titin Yakubu Gowon a garin na Jos, lokacin da aka sace na’ura mai kwkwalwa mallakar daya daga cikin shugabannin jam’iyyar a jihar.

Bayan na’urar, an sace wasu kayayyakin mallakar Ishaku Chuntai, babban daraktan gudanarwa na jam’iyyar PDP a jihar Filato. Kayan sun hada da wani alkalami na zinare da kayan shayi ma su tsada.

Ɗan sanda mai gabatar da kara Daniel Longwal, ya shaidawa kotun cewa wadanda aka gurfanar sun hada baki wajen balle ofishin Chuntai tare da yin awon gaba da na’ura mai kwakwalwa da alkalamin zinare da kuma kayan shayi da darajar kudinsu ta kai naira 135,000.

Daniel Longwal ya sanar da kotun cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da aikin sauya makulli da za a yi a ofishin Chocho wajen samun damar shiga tare da yi ma sa sata.

Wanda hakan ya saba da sashe na 53, 273 da 231 na kundin hukuncin aikata laifuka a jihar Filato.

A ƙarshe alkalin kotun ya amince da bayar da belin wadanda ake kara a kan kudi naira 50,000 kowanne mutum da kuma wakili da zai tsayawa kowannensu tare da daga sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga watan Satumba.

Tsohon Shugaban jam’iyyar PDP Yakubu Chocho

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here