Ashe tsimin Madagascar ba ya warkar da cutar coronavirus?

0
2582

Gwamnatin Najeriya ta ce babu alamun tsimin da aka karbo daga kasar Madagascar zai warkar da cutar coronavirus kamar yadda aka yi ikirari.

Ministan lafiya na kasar nan Osagie Ehanire, ne ya sanar da haka, yana mai cewa cibiyar binciken magunguna ta kasar ta bayyana rahoton binciken da ta yi, inda ta ce maganin na Madagascar na da sinadaran da za su iya rage yawan tari ne amma ba waraka ce ga cutar Covid 19 ba.

A watan Afrilu ne shugaban kasar Madagascar Andry Rajoelina ya kaddamar da wannan tsimi, da ya yi ikirarin yana warkar da cutar coronavirus.

Hukumar lafiya ta duniya ta yi kashedi a kan shan maganin da Madagascar ta samar ba tare da sa idon likita ba.

Kasar Madagascar da ke tsibirin tekun India, ta baiwa kasashen Afrika wannan magani da ta ce yana kawo waraka ga cutar coronavirus.

A farkon wannan wata, Madagascar ta sake kakaba dokar takaita zirga zirga a yankin Analamanga sakamakon karuwar wadanda cutar coronavirus ta harba.

Ta kuma bude karin cibiyoyin jinyar cutar da ke ci gaba da yaduwa a sa ssan duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here