Ba Duka Mace-Macen Kano Ke Da Alaka Da Korona Ba –Ganduje

0
93

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje,  ya musanta rahoton kwamitin gwamnatin tarayya da ya gano cewa cutar korona ce ta yi ajalin kashi 50 zuwa 60 cikin 100 na mutanen da suka mutu a baya bayan nan.

Musantawar ya fito ne daga bakin Abba Anwar, Kakakin Gwamna Ganduje a wata sanarwa da ya fitar,  inda ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin yin bincike kan yawan mace-mace da aka samu a lokacin bullar annobar korona ya gano cewa kusan kashi kashi goma sha shida ne cikin dari ne suka mutu sakamakon korona.

Ministan Lafiya na Nijeriya, Osagie Ehanire a makon da ya gabata ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa binciken da tawagar gwamnatin tarayya ta gudanar game da ƙaruwar mace-mace a jihar Kano ya nuna cewa mutum 979 ne suka mutu a kwanan nan sanadin mace-macen da ba a saba gani ba a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here