‘Ba Sulhu’: Ƴan daba a ƙwaryar birnin Kano

0
2443

‘Ba Sulhu’ sunan gungu ko dabar wasu ‘yan daba ko ‘yan ta’addar matasa ne da su ka harhaɗu daga unguwanni su ke aikata rashin mutuncin su a ƙwaryar Kano.

An ce matasan, waɗanda da ma can ‘yan daba ne a unguwanni su, su na haɗuwa su haɗa kan su a wuri guda a matsayin tafiya guda.

An ce su na haɗuwa ne a wani keɓaɓɓen wuri kamar filin Sukuwar Dawakai (wani fili ne a Kano da ake sukuwar dawakai da ƙwallo, filin a keɓe ya ke, duk da yake yanzu gine-ginen gidajen masu kuɗi da manyan shaguna ya mamaye shi).

Su kan tattaru, su fito ‘operation’ zuwa unguwa ko wata kasuwa ko wani wuri da su ka ware, su ɗauki muggan makamai su dira kasuwar ko unguwar, su kori mutane, su shiga sace-sacen kuɗi da ƙwacen waya. Su kan sari mutumin da zai kawo musu cikas, idan tsautsayi ya zo, har da kisa.

Su kan yi tafiyar sama da kilomitoci goma sha biyar har sama da hakan, su na cin karen su ba babbaka ba tare da tarnaƙi daga jami’an tsaro ba.

Su kan farmaki motocin Keke Napep (A Daidaita Sahu), musamman mai ɗauke da fasinjoji, su shisshiga su zare wuƙa su nuna wa fasinjan, su karɓe masa waya. Kuma su kan iya tare tituna su na yin wannan ta’addancin nasu.

Kwanan nan su ka kawo farmaki unguwar mu, Fagge, har tsakiyar layin mu, har ta ƙofar gidan mu, su ka wuce su ka yi abin da su ke so, su ka tafi.

‘Yan kwamiti ne su ka iya korar su, sannan daga baya ‘yan sanda masu bindigogi su ka zo wajen, bayan sun tafi.

Sannan ranar Talatar da ta wuce ne hukumar ‘yan sanda ta Jihar Kano ta yi sanarwar kama wasu ‘yan wannan ƴungiya su sama da goma sha biyar a gidajen rediyo a Kano.

Duk tsarin da ‘yan wannan ƙungiyar ta ‘Ba Sulhu’ su ke yin ta’addancin su iri ɗaya ne da na irin ƙauyukan Zamfara da Katsina; bambancin kawai, su ‘Ba Sulhu’ da adduna, ko fate-fate ko wuƙa da sauran su su ke harkokin su, su kuma waɗancan da bindigogi.

Abin tsoron, idan ana haka, wata rana waɗannan matasa kan iya samun bindigogi. Me ake zato ka iya faruwa?

 

Kabiru Yusuf (Anka) marubuci ne a Kano

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here