Babu gaskiya a cikin jita-jitar da ake akan Sanata Gaya ya kwato Yunusa Yellow – Idris Ahmad

1
5344

Fitaccen dan gwagwarmayar rajin kare hakkin dan adam a shafukan zada zumunta kuma mazaunin ƙasa Ingila, Dakta Ahmed Idris, ya bayyana cewa babu gaskiya akan jita-jitar da ake na Sanata Kabiru Gaya ya kwato Yunusa Yellow.

Ahmed Idris ya bayyana hakan ne a shafinsa na fasebuk a safiyar yau alhamis.

“Assalamu alaikum Jama’a. Barkanmu da war haka. Yanzu na gama waya da Madugun tafiya, Dr. Auwal Mustapha Imam. Yayi mini cikakken bayanin cewa lallai har yanzu hukuma suna tsare da bawan Allah Yunusa Yellow. Babu gaskiya a cikin wani jita-jita da akeyi wai Sanata Kabir Gaya ya kwato wa Yunusa yancinsa”

“Sai dai kuma, mun sami izini daga gun shi Yunusa Yellow, domin daukaka qara ranan Juma’a idan Allah ya kaimu. Allah yasa mudace. Allah yayi mana jagora. Amin”

Idan za a iya tunawa dai a cikin watan Mayu ne wata babbat Kotu ta yanke wa Yunusa Yellow hukuncin daurin shekara 26 a gidan Yari.

Babbar kotun da ke zama a birnin Yenagoa da ke jihar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Dahiru da aka fi sani da Yunusa Yellow daurin zaman gidan kaso na shekara 26 bisa samun shi da laifin safara da cin zarafin Ese Oruru.

A shekarar 2015 ne dai mahaifan Ese Oruru suka yi zargin Yunusa Yellow da yin ‘garkuwa’ da yarsu, ya kuma kai ta jihar Kano inda ya tilasta mata aurensa har ma aka samu juna biyu.

Wannan batun dai ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin ‘yan kudu da arewacin Najeriya, musamman bayan da ta bayyana cewa Ese Oruru ta musulunta inda ta bar addininta na Kirista.

Ese Oruru dai ta zama Aisha bayan da ta musulunta amma daga baya sai rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kubutar da Ese Oruru mai shekara 13.

Alkalin kotun dai ya ce ba a samu Yunusa Yellow da laifin na farko ba na garkuwa da mutum, to sai dai ya ce an same shi da laifin safarar kananan yara da yin jima’i ba tare da amincewa ba da cin zarafi.

Mai shari’a Jane Iyang daga karshe ya yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin zaman gidan kaso na shekara 26.

To sai dai bisa doka, Yunusa Yellow na da hurumin daukaka kara.

1 COMMENT

  1. Tonda anyenkewa Yunusa yellow hukonci. To a’ina a’kakwana gamai da Mutanen da suka sace yara daka Kano suka Kai su Kudu, suka canja musu ad’dini da sunayen su?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here