Bai kamata a harbi ko kashe kowa ba akan zanga-zanga – Atiku Abubakar

0
206

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa bai kamata jami’an tsaron ƙasar nan su ɗauki matakin harbi ko bindigewa ba ga masa zanga-zangar ƙin jinin rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a ƙasar nan wato SARS ba.

Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a shafinsa na fasebuk.

“Bai kamata a harbi wani ko kashewa ba saboda kawai yana zanga – zanga akan nuna ƙyamar rashin gaskiya” In ji Atiku Abubakar.

A jiya ne dai babban aifeton ƴan sandan ƙasar nan Mohammed Adamu, ya soke rundunar ta SARS.

Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar nan.

Sai dai duk da sanarwar da Sufeto Janar na ƴan Sandan ya bayar na rushe rundunar SARS, har yanzu zanga-zangar nuna ɓacin rai ba ta dakata ba sakamakon sababbin buƙatun da al’ummar ƙasar nan suka miƙawa gwamnati.

Ƴan Najeriya dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.

Kalaman na Atiku Abubakar na zuwa ne ƙasa da sa’o’i huɗu da shugaba Muhammadu Buhari ya ce soke rundunar ta SARS matakin farko ne a sauye-sauye masu tsauri da zai aiwatar kan aikin ƴan sanda domin tabbatar da cewa jami’an tsaro sun yi aikin da ya dace da kare rayuka da dukiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here