Ban taɓa nadamar goyan bayan zaben shugaban ƙasa Buhari ba – Bola Tinubu

0
895

Jagoran Jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu yace ko da sunan wasa baya nadamar goyan bayan zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015 da 2019.

Yayin da yake mayar da martani kan zargin cewar yayi nadamar marawa Buharin baya da kuma kashe naira biliyan 35 wajen yakin neman zaben shugaban kasar saboda yadda aka rusa zaben shugabannin jam’iyyar, Tinubu yayi watsi da rahotan wanda ya bayyana shi a matsayin cewar yunkuri ne na raba kan ‘Yan Jam’iyyar APC.

A sanarwar da mai magana da yawun sa Tunde Rahman ya rabawa manema labarai, Jagoran APCn yace ba mutum guda ne ya zabi Buhari ya zama shugaban kasa ba, domin kuwa akasarin ‘Yan Najeriya ne suka zabe shi, saboda haka babu dalilin da Tinubu zai ce shi ya zabe shi.

Sanarwar tace Tinubu da sauran Yan siyasar Najeriya na gari tare da al’umma sun goyi bayan Buhari daga kowanne sako na kasar a shekarar 2015 da 2019 saboda suna da yakinin babu wanda ya fi shi cikin ‘yan takarar da ake da su, saboda haka baya nadamar yin haka.

Tinubu yace ganin yadda labarin yayi tsokaci kan yadda tsohon Gwamna Akinwumi Ambode ya gaza samun tikitin wa’adi na biyu ya nuna inda zargin da aka masa ya fito.

Sanarwar tace Tinubu ya manta da zaben shekarar 2019 wanda ya riga ya wuce, kuma yanzu haka ya mayar da hankalin sa a gaba, kamar yadda Lagos da sabon Gwamnan ta Babajide Sanwo-Olu suka yi wajen gudanar da shugabanci na gari da jama’a ke alfahari da shi.

Rahman yace Bola Tinubu da Sanwo-Olu na da dangantaka mai kyau a tsakanin su, sabanin yadda wasu ke koka rin nunawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here