Ban yi wa Buhari yakin neman zaben shekarar 2015 ba – Sambo Dasuki

1
4211

Tsohon mai baiwa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro Kanar Sambo Dasuki yace bai yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari yakin neman zabe a karkashin Jam’iyyar APC ba tsakanin shekarar 2011 zuwa 2015.

Wata sanarwar da Dasuki ya rabawa manema labarai mai dauke da sanya hannun sa, Kanar Dasuki yace ya taka rawa ne kawai kafin zaben shekarar 2011 lokacin da ake neman kulla kawance tsakanin Jam’iyyar ACN da ANPP da kuma CPC.

Dasuki yace yunkurin sa na ganin an samu nasarar kawancen yak are lokacin da aka gudanar da zaben shekarar 2011, inda ya karkade hannayen sa daga harkokin siyasa.

Tsohon mai bada shawarar ya musanta rahotan cewar ya yiwa Buhari yakin neman zabe a boye lokacin da yake aiki da shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Kanar Dasuki yace a karon farko yayi watsi da rahotan, amma kuma daga bisani yace ya zama wajibi ya fito fili domin karyata labarin ganin yadda ake neman bata masa suna.

Tsohon hafsan sojin yace lokacin da shugaba Jonathan ya masa tayin mukami a gwamnatin say a shaida masa cewar yana da alaka da shugaba Muhammadu Buhari na CPC da Bola Ahmed Tinubu na CAN da Ogbonaya Onu na ANPP da kuma wasu jiga jigan yan adawa a lokacin.

Kanar Dasuki ya shaidawa Jonathan cewar ba zai ci amanar sa ba, kuma hakan yayi lokacin da suka yi aki tare.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here