Batun Tsaro Da Cutar Korona Na Bukatar Addu’o’i –Gwamna Fintiri

0
1576

Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri a ranar Lahadi ya shawarci shugabannin addini da su tsananta addu’o’i domin kawo karshen ‘yan bindiga da masu garkuwa da jama’a da kuma annobar cutar korona.

Gwamna Fintiri ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shugabannin gidauniyyar ‘Zawiyyatu Dariqatit Tijjaniyat Foundation of Nigeria’ reshen jihar Adamawa a garin Yola.

Gwamnan wanda mataimakinsa na musamman kan muhimman ayyuka, Alhaji Bamanga Nuhu, ya wakilce shi, inda ya ce matsalar garkuwa da jama’a da ta’addanci da yake aukuwa da kuma annobar cutar korona, suna daga cikin manyan matsalolin da suka hana ci gaban kasar.

Gwamna Fintiri ya tabbatar da cewa; a shirye yake ya taimakawa kungiyoyin addini domin wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.

A karshe ya taya sabbin shugabannin murna, tare da jan hankalinsu wajen bada lokacinsu da basirarsu wajen habbaka gidauniyyar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here