Bayan Sanata Ndume Zai Tsayawa Maina, Kotu Za Ta Duba Yiwuwar Sake Bada Belinsa

0
87

Babbar kotun tarayya dake Abuja, a ranar Litinin ta ce za ta duba yiwuwar bai wa tsohon shugaban tawagar hukumar Fensho (PRTT), Abdulrasheed Maina beli.

Kotu za ta sake duba sharuddan belin ne wata takwas da bada belinsa wanda ya kasa cikawa.

Alkali Okon Abang a hukuncin da ya yanke, ya ce bisa tausayawa ne zai bai wa Maina Beli, musamman duba da yadda ya kawo dan majalisar Dattawa mai ci  a kasarnan wanda zai tsaya masa.

Rahotanni sun bayyana cewa; Lauyan da yake tsayawa Maina, Joe Gadzama, SAN, a ranar 23 ga watan Yuni ne ya shaidawa kotun cewa Sanata Ali Ndume da yake wakiltar Borno ta Kudu na son tsayawa Maina.

Gadzama ya ce duk da sun cika wannnan sharadin, sai dai takardar shaidar gida a Abuja na wanda zai tsaya masa, ba sunan Sanatan bane a jiki.

Lauyan ya ce sunan wani mutum mai suna Lawan Ahmed  a jiki, wanda shi ne asalin mai muhallin.

Sai dai Gadzama, ya ce amma yanzu Ndume ne ke da muhallin. Ya ce akwai takarda (Exhibit G2)  dauke da sa hannun Daraktan muhalli na Abuja, FCTA G. Bawa, da ya rubutowa Magatakardar kotun domin tabbatarwa.

Sanata Ndume, wanda shi ne shugaban Kwamitin Sojoji na majalisar, a ranar 24 ga watan Yuni ya tabbatar da cewa zai tsayawa Maina a wata sanarwa da ya fitar. Ya ce sai da ya kwashe wata shida yana tunanin ya tsayawa Maina din.

EFCC a ranar 25 ga Oktoba, suka gurfanar da Maina da dansa Faisal da kuma kamfaninsa Common Input Property and Investment Ltd inda ake zarginsa da aika laifuka takwas da ya hada da hulda haramtattun kudi, wanda ya karyata zargin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here